A ranar 15 ga Agustan 2021 ce kungiyar Taliban ta kwace mulkin Afghanistan, bayan sojojin Amurka sun fice daga kasar.
Sojojin kawancen Amurka sun shafe shekara 20 a Afghanistan, inda suka kifar da gwamnatin Taliban da ta shekara shida tana jagorantar kasar daga 1996 zuwa 2001.
- Yadda Taliban ke yaki da shan miyagun kwayoyi a Afghanistan
- ’Yan Taliban sun watsa taron mata masu zanga-zanga
Taliban ta fara ne da kaddamar da hari a Kudancin Kandahar, daga nan ta ci gaba da karfafa har ta kwace fadar gwamnatin kasar a ranar 15 ga watan Agusta, wanda ya sa Shugaban Kasar na wancan lokaci, Ashraf Ghani, tserewa tare da cewa kungiyar ta yi nasara.
Bayan cika shekara daya da dawowar kasar karkashen mulkin kungiyar, Aminiya ta yi nazari tare da tattaro wasu muhimman abubuwan da suka faru a kasar a tsawon wata 12 da suka shude:
Karbe birnin Kabul
A daidai lokacin da Amurka da kawayenta suka fara janye sojojinsu daga Afghanistan ne Taliban ta kaddamar hare-haren karshe na sake kwace mulkin kasar bayan shekara 20.
A watan Agusta mayakan kungiyar suka kaddamar da wani gagarumin hari, suka ci gaba da nausawa tare da karbe muhimman garuruwa a sassan kasar cikin kwana 10.
A ranar 15 ga watan Agustan 2021 suka kwace Kabul, fadar gwamnatin kasar, wanda ya sa Shugaba Ashraf Ghani tserewa zuwa birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Turmutsutsi a filin jirgin Kabul
Bayan nan ne dubban ’yan Afghanistan da mazauna kasar, cikin firgici suka yi tururuwa zuwa filin jirgin saman Kabul domin ficewa daga kasar.
Amurka ta rufe asusun ajiyar gwamnatin Afghanistan da ke dauke da Dala biliyan bakwai, sannan sannan masu ba da agaji daga ketare suka daina ko rage taimakon da suka saba bai wa kasar.
Ficewar Amurka kacokan
Amurka da kawayenta sun yi ficewar karshe daga Afghanistan ne ta filin jirgin Kabul, inda suka kwashe jami’ansu da ’yan kasar Afghanistan da suka yi aiki tare da su.
Lamarin ya sanadiyar mutuwar wasu daga cikin mutane da suka yi dandazo suna kokarin makalewa a jirgin Amurka na karshe da zummar ficewa daga kasar, ciki har da jami’an tsohuwar gwamnati da wadanda suke taimaka wajen yakar Taliban da iyalansu.
A ranar 26 ga Agusta aka samu tashin bam da ya halaka sama da mutum 100, ciki har da wasu jami’an Amurka 13.
Mayakan ISIS da ke Afghanistan da Pakistan, wato kishiyar Taliban, sun dauki alhakin kai harin.
Kwana hudu bayan nan, 30 ga watan Agusta, Taliban ta yi murnar ficewar dakarun Amurka gaba daya daga Afghanistan.
Dawowar tsattsauran ra’ayin addini
Duk da ikirarin Taliban na kawo karshen danniya, amma alamu su nuna tsugune ba ta kare ba.
A watan Satumba kungiyar ta kaddamar da sabuwar gwamnatin wucin gadi, wadda a ciki ta bai wa masu tsattsauran ra’ayi muhimman mukamai ba tare da bai wa mata wata dama ba.
Kungiyar ta dawo da Ma’aikatar Inganta Kyawawan Dabi’u da Hana Aikata Laifuka, wadda aka dakatar.
Wannan mataki ya haifar da zanga-zanga a birnin Kabul da Herat, inda aka harbe mutum biyu har lahira.
ISIS ta kai hari masallatai
A watan Oktoba kungiyar ISIL (ISIS) ta kai hari a wani masallacin Shi’a da ke Kandahar a lokacin da ake tsaka da Sallar Juma’a, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 60.
Harin wanda shi ne mafi muni tun bayan ficewar dakarun Amurka daga kasar, ya auku ne mako guda bayan harin kunar bakin waken da ya kashe mutane da dama a wani masallacin Shi’a a Arewacin Kunduz.
Tattaunawar Norway da Taliban
Dawowar Taliban ya jefa Afghaninstan cikin matsin tattalin arziki, saboda rashin samun tallafi daga kasasshen duniya.
A sakamakon haka ne kasar Norway ta gayyaci gwamnatin Taliban zuwa Oslo, babban birnin kasar, domin tattaunawa.
Taliban ta tura wakilai don tattaunar a Oslo, inda Amurka da kasashen Turai suka yi amfani da damar wajen duba yiwuwar tura tallafinsu kai-tsaye ga al’ummar Afghanistan din.
Hana ’yan mata zuwa makaranta
Bayan an sake bude makarantu a watan Maris, hukumomin Taliban suka haramta wa ’yan mata zuwa makarantun sakandare.
Sun kuma wajabta wa ma’aikatan gwamnatin kasar ajiye gemu.
Tilasta wa mata rufe jikinsu
A watan Mayu gwamnatin ta kafa dokar wajabta wa mata da budare sanyan hijabai da rufe fuskokinsu kafin su fita waje.
Hukumar Hisbah ta kasar ta bayyana ce ta fi son mata su rika zaman gida.
Mata masu gabatar da shirye-shiryen talabijin da wasunsu na daga cikin hadafin dokar, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a sassan duniya.
Kazalika, an haramta wa mata yin tafiya mai nisa su kadai, ko zuwa wuraren shakatawa face a ranakun da aka haramta wa maza shiga wuraren.
Girgizar kasa
Sama da mutum 1,000 sun rasu, wasu da dubbai kuma suka rasa muhallansu bayan mummunar girgizar kasar da ta auku a ranar 22 ga watan Yuni a iyakar kasar da Pakistan.
Iftila’in ya haifar da babban kalubale ta bangaren aikin agaji ga gwamnatin Taliban, wadda kasashen duniya ba su aminice da halascinta ba.
Daga bisani kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun shigo sun taimaka wa kasar da kayan abinci, magunguna da sauransu.
Kashe jagoran Al-Qaeda
A ranar 2 ga Agustan bana, Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden ya sanar da kashe jagoran kungiyar Al-Qaeda, Ayman al-Zawahiri, a wani harin jirgi mara matuki a maboyarsa da ke Kabul.
Amurka na zargin al-Zawahiri da kitsa harin da aka kai wa Amurka ranar 11 ga Satumbam 2001.
Taliban ta yi tir da harin na Amurka, amma ba ta tabbatar da mutuwar al-Zawahiri ba, tana mai cewa tana kan binciken ikirrain da Amurka ta yi.
Ana kallon Taliban a matsayin mai tsattsauran ra’ayin Islama da kuma alaka da kungiyar Al-Ka’ida – wadda ake zargi da harin ranar 11 ga watan Satumba, 2001 a Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da ke Amurka.