✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da muka tattauna da Tinubu kan rikicin Mali —Jonathan

Tinubu ya gana da Jonathan a fadar shugaban kasa a ranar Talata.

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karbi wasu bayanai kan wasu al’amuran siyasa a yammacin Afirka daga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Jonathan dai shi ne wakili na musamman na Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) a kasar Mali.

Tsohon shugaban kasar ya ce ya je fadar shugaban kasa ne domin bayyana wa Shugaba Tinubu sakamakon tattaunawa da sauran mambobin kungiyar dattawan Afirka ta Yamma, wadda yake shugabanta.

“Na zo ne domin na yi wa shugaban kasa bayanin yadda ayyuka ke tafiya. Ka san ni ne mai shiga tsakani na ECOWAS a Mali kuma Shugaban Kungiyar Dattawan Afirka ta Yamma.

“Don haka, akwai wasu batutuwan da suka shafi nahiyar da kuma yankin da nake tattaunawa da shugabanni daban-daban,” in ji shi.

Jami’an tsaron kasar Mali a ranar Lahadi 11 ga watan Yuni, sun kada kuri’a gabanin zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin da aka shirya gudanarwa a ranar 18 ga watan Yuni.

Ana dai kallon kuri’ar raba gardamar a matsayin wani babban cigaba a jerin zabukan da aka shirya gudanarwa a watan Fabrairun 2024.