✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da muka tattauna da Obasanjo — Sheikh Gumi

Ya kamata gwamnati ta yi wa ’yan bindiga afuwa wadanda suka shirya tuba.

Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana yadda ta kasance yayin ganawarsa da tsohon Shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo a ranar Lahadi.

Aminiya ta ruwaito cewa, Sheikh Gumi da wasu shugabannin addinai sun kai wa tsohon shugaban kasar ziyara har dakin karatunsa da ke Abeokuta, babban jihar Ogun.

Bayan ganawar ta su, dukkaninsu sun yi wa manema labarai jawabi inda Sheikh Gumi ya sanar da gabatar wa da tsohon shugaban kasar goron gayyata zuwa Jihar Kaduna, domin ci gaba da tattaunawa a kan matakan da za su kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi kasar musamman yankin Arewa.

A cewar shehin malamin, sun bukaci a tanadi wasu kotuka na musamman da za su rika jibintar lamarin ’yan daban daji, masu garkuwa da neman kudin fansa da kuma dauka da yawo da makamai ba bisa ka’ida ba.

A cikin shawarwarinsu, Obansanjo da Gumi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta yi wa matsalar tsaro riko a duk iyakokin yankin Afirka ta Yamma domin magance matsalar baki daya.

Sannan sun gargadi ’yan Najeriya da su guji jifan junansu da zargi ko kabilanci da nuna wariya tare da neman a rika girmama juna da kuma muntatawa a dukkan zamantakewa.

Kazalika, Obasanjo da malamin sun nemi Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi wa ’yan bindigar da suka rungumi zaman lafiya afuwa.

A cewar Obasanjo, “ya kamata gwamnati ta yi wa ’yan bindiga afuwa wadanda suka shirya fita daga daji da ajiye makamai da kuma daina miyagun laifuka.”

“A gyara halayyarsu sannan a koya musu ayyuka da kuma basu jari ya zama sun samu abin dogaro da kai,” in ji Obasanjo

“Muna kuma kiran gwamnatin a kan kada ta sake ta rangwantawa duk wasu ’yan bindiga da suka ci gaba da tayar da zaune a kasar nan.”

Gumi wanda ya isa gidan tsohon Shugaban Kasar da misalin karfe 11.00 na safe tare da tawagarsa ta shugabannin addinai, sun yi bakwana da gidan da misalin karfe 4.00 na yamma.

Tawagar da sheikh Gumi ya jagoranta ta kunshi Farfesa Usman Yusuf, Mallam Tukur Mamu, Dokta Umar Ardo, Dokta Ibrahim Abdullahi, Honarabul Suleiman Gumi, Alhaji Suleian Yakubu da kuma Mallam Buba Muhammad.

Sauran ’yan tawagar sun hada da Oba Babajide Bakare, Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya ta jihar Ogun;Tunde Akin-Akinsanya, Babban Limamin Egbaland; Sheikh Sa’adallah Alade Bamigbola, Cif Kenny Martins, Cif Ola Babajide Jaiyebo, Rabaran Tony Ojeshina, da sauransu.

%d bloggers like this: