✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da malaman Sakkwato suka gaya wa gwamnati kan batanci

An kashe mutum daya an jikkata da dama a yamutsin batanci a Sakkwato

Malaman Islama a Jihar Sakkwato sun shawarci gwamnati a matakin jiha da tarayya su kafa dokar yanke hukuncin kisa kan kowane irin nau’in batanci a fadin Najeriya.

Limaman masallatan Juma’a na Jihar Sakkwato ne suka bayyana haka bayan rikicin da ya barke kan batanci ga Manzon Allah (SAW) da wata daliba a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke jihar, Deborah Yakubu, ta yi.

Daya daga cikin malaman da suka halarci zaman da gwamnatin jihar ta kira ranar Juma’a, ya shaida wa Aminiya cewa sun sun yi ittifakin cewa ya kamata dokar da za a kafa ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin ya yi batanci.

A lokacin zaman da Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal ya jagoranta, limaman sun bukaci a wajbta wa duk daliban manyan makarantu rubuta takardar rantsuwa cewa za su mutunta addinin juna.

Rikicin batanci: An kashe mutum, an jikkata da dama

Akalla mutum daya ya rasu wasu da dama sun jikkata a rikicin da ya barke kan batancin da wata daliba, Deborah Yakubu, ta yi wa Fiyayyen Halitta a Kwalejin Ilimi na Shehu Shagari da ke Jihar Sakkwato.

Tarzomar, wadda ta soma daga zanga-zangar lumana ta neman a sako wadansu mutane da ’yan sanda suka tsare kan zargin kashe Deborah da ta yi batancin, ya rikide zuwa kone-kone a sassan garin Sakkwato.

A kan haka ne gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita gaba daya da na tsawon awa 24, domin dakile yaduwar rikicin.

Wannan ya biyo bayan wani zama da gwamnan jihar, Aminu Tambuwal ya yi da malaman addini da shugabannin hukumomin tsaro a ranar Juma’a kan kisan dalibar da aka yi ranar Alhamis.

Gwamnan ya kira zaman ne a ranar Juma’a domin dakile hare-haren daukar fansa bayan kaddamar da mai batancin da daliban kwalejin suka yi, kan batancin.

Zanga-zanga ta koma tarzoma

Masu zanga-zangar da taka yada gayyatarta ta shafukan sada zumunta sun fara ta ne a ranar Asabar da safe daga shataleteln Zabirah Mall da ke garin Sakkwato, dauke da kwalaye.

Sun daga kwalayen neman a sako wadanda jami’an tsaro suka tsare.

Daga bisa adadin masu zanga-zangar ya yi ta karuwa wasu a kan babura, suna ta kabbara, suka yi tattaki zuwa Fadar Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar, amma jami’an tsaron hadin gwiwa da ke tsaron fadar suka tarwatsa su.

Wakilinmu ya ziyarci wajen, inda ya ga an kona tayoyi a kan yawancin hanyoyin garin na Sakkwato, musamman hanyoyi da ke zuwa Fadar Sarkin Musulmi.

A protester injured

Aminiya ta ga yadda aka kirge jami’an tsaro a muhimman wurare a birnin Sakkwato, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sakwkato,Kamal Okunlola.

Wani daga cikin masu zanga-zangar ya shaida wa wakilinmu cewa jami’an tsaro sun harbi mutane da dama, sannan an, an kona motoci tare da fasa shagunan mutane an kwashe kaya, musamman a kan babban titin Emir Yahya da ke garin na Sakkwato. 

Ranar Asabar da dare, Shugaban Darikar Katolika da ke Sakkato, Bishop Mathew Hassan Kukah ya karyata ji-ta-ji-tar da ake ta bazawa cewa masu zanga-zangar sun kona gidansa.

Bishop Kukah ya shaida wa kafar yada labarai ta The Cable, cewa babu kamshin gaskiya a labarin da ke ta bazawa. 

Aminiya ta ga yadda aka girke jami’an tsaro domin kare wuraren ibada da sauran muhimman wurare abirin Sakkwato, inda aka rufe shaguna kan babban titin Ahmadu Bello da ma wasu wurare.

Muna shawo kan lamarin –’Yan sanda

Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Sakkwato, Kamal Okunlola, ya tabbatar wa Aminiya cewa hukumomin tsaro na yin duk mai yiwuwa na shawo kan al’amarin..

Ya ce an girke jami’an tsaro a sassan jihar sannan ya bukaci jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu a cikin gidajensu, a tsawon lokacin dokar hana fitar da gwamantin jihar ta sanya.