✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ke tsorata mu game da zabe mai zuwa -Sheikh dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya zanta da Aminiya inda ya yi bayani game da zabe mai zuwa da kuma matsalolin…

Sheikh Dahiru Usman BauchiFitaccen malamin addinin musuluncin nan Sheikh dahiru Usman Bauchi ya zanta da Aminiya inda ya yi bayani game da zabe mai zuwa da kuma matsalolin tsaro a Najeriya.  Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Me za ka ce game da yadda wata kungiya ta fito a jarida tana nuna cewa tana  tare da shugaba Jonathan da sunan Tijjaniya Awareness?
Sheikh dahiru: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukacin Sarki. Hakika kwanakin baya akwai wata kungiya mai suna Tijjaniya Awareness iniatibe forum ta hada hotona da na shugaban kasa da sunan cewa wai tana wa shugaba Goodluck Jonathan kamfen. Babu wani dan Tijjaniya na gaskiya da zai tallata shugaba Jonathan a Najeriya, saboda haka muna nisanta kanmu da wannan kungiya ta bogi. Kuma babu mamaki wadansu ‘yan siyasa ne suke amfani da wannan kungiyar domin kawo rudani a tsakanin al’umma. Kuma su suka dauki nauyinsu domin shiga kafafen watsa labarai da wannan farfaganda. Saboda haka idan su ‘yan Tijjaniya na gaskiya ne su fito fili mu gansu.
‘Yan darikar Tijjaniya ba su da wani aiki sai zikiri da hailala da salatin Annabi, wadannan su ne manufofin ‘yan Tijjaniya, ba shiga harkokin siyasa ba. Nasha fada a baya, ni ba dan kwangilar  yayata shugaba Jonathan ba ne.
 Aminiya: Mene ne sakonka ga al’umma game da babban zabe da ke tafe?
Sheikh dahiru: Ina kira da babban murya ga al’ummar Najeriya da kowa da kowa ya fito ya kada kuri’arsa a ranar zabe, domin ta haka ne za a fitar da Najeriya daga halin da take ciki. Ni ba dan siyasa ba ne, amma abin da ya kamata al’umma su yi shi ne su zabi gaskiya a ranar zabe. Babban tsorona shi ne idan aka zabi Jonathan a zaben 2015 ba za a zauna lafiya a Arewa ba. Idan kuma aka zabi Janar Muhammadu Buhari mutanen kudancin Najeriya ba za su bari a zauna lafiya ba. Fatanmu a nan shi ne a yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.
Aminiya: Da gaske ne ka ce shugaba Jonathan da amurkawa ne suke kashe mutane a Najeriya?
Sheikh dahiru: Wannan magana ba gaskiya ba ne kuma ban fadi haka ba, abin da na fada shi ne, hakkin gwamnati ne ta kare rayuka da dukiyoyin al’umma, duk gwamnati da ta gagara samar da tsaro to tabbas ba ta da amfani a wajen al’umma. Don haka muna ganin watakila gwamnati tana da hannu dumu-dumu a wannan rikici wanda ya yi sanadiyar lakume dimbin rayukan al’umma a wannan shiyya na Arewa maso gabas.
Akwai wani tsohon soja da muka tattauna da shi, ya bayyana mini cewa idan aka ba shi dama zai iya kawar da ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa da ke jihar Borno. Na fada, zan kuma sake fada, gwamnatin Najeriya tana wasa da rayukan al’umna. Allah zai kawo mana karshen wannan matsala wanda ya zamo kadangaren bakin tulu ga gwamnatin Najeriya.
Mun bada wadansu addu’o’i da yanzu haka ana cigaba da yi, kuma nan da makonni uku masu zuwa muna fata abubuwa za su canza a Najeriya. Masu mana kulle-kulle Allah zai tona musu asiri.
Kuma za mu cigaba da fadan gaskiya babu wanda ya isa ya rufe mana baki, yanzu gwamnati ta cire rubutun ajami a jikin sabuwar Naira 100, idan Allah Ya kawo wata sabuwar gwamnati za mu tilasta mata sai ta mayar da rubutun da aka cire.
Aminiya: Wane  tsokaci za ka yi game da yadda aka gudanar da bukukuwan maulidi na bana?
Sheikh dahiru: An gudanar da bikin maulidi na bana cikin kwanciyar hankali, saboda haka muna godiya ga Allah. Akwai dimbin mutanen da suka halarci wajen maulidin wanda aka saba gudanarwa a dandalin Ibrahim Badamasi Babangida a cikin garin Bauchi. Daga cikin kasashen da suka halarci wajen maulidin akwai mutanen Ghana da Kamaru da Nijar da Senigal da Maroko da Chadi da Gini, da sauran wadanda suka fito daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka. Gwamnonin jihohin Zamfara da Jigawa sun taimaka mana, kuma gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda  ya halarci wajen taron, sannan ya ba mu gudunmawa.