✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da EFCC ta ce kan zargin kwace N400bn a gidan Tinubu

EFCC ta ce babu gaskiya a labarin kanzon kuregen da ke cewa jami'anta sun kai samame a gidan Tinubu, ballantana su kama makudan kudaden da…

Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bara game da labarin da ke yawo cewa ta kama tsabar sabbin kudi Naira biliyan 400 a gidan dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu.

EFCC ta ce babu gaskiya a labarin kanzon kuregen da ke cewa jami’anta sun kai samame a gidan Tinubu, ballantana su kama makudan kudaden da ake rade-radi a kafofin sada zumunta.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, a sanarwar da hukumar ta fitar, ya ce, “Karya ne labarin da ke yawo cewa EFCC ta kai samame gidan dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC a zaben da ke tafi, ta kama tsabar kudi Naira biliyamn 400.”

Sanawar mai taken ‘‘EFCC Ba Ta Kai Samame Gidan Tinubu Ba’, ta ci gaba da cewa, “EFCC ba ta kai wannan samame da ake yadawa ba, kuma tara kira ga jama’a da su yi watsi da labarin karyar.”

Hukumar ta fitar da sanarwar ce, bayan kaofofin sada zumunta sun yi ta bazawa cewa jami’an EFCC bisa umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sun kai samame a gidan Tinubu inda suka kama tsabar kudi Naira biliyan 400 na sabbin takardun kudi.