Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta bayyana sakamakon binciken da ta yi kan harin da aka kai wa Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno. —Sojoji
A makon jiya ne aka bude wa motocin gwamnan wuta a hanyar Baga, inda ya zargi soji da zagon kasa ga yunkurin gwamnati na kawo karshen ta’addancin Boko haram a yankin Arewa maso Gabas.
Sai dai Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta ce binciken da ta gudanar ya gano babu kamshin gaskiya a zargin dakarun sojin da ke aiki a yankin.
Kakakin Hedikwatar Tsaro Manjo Janar John Enenche, ya bayyana haka a tattaunawarsa da gidan talbijin na Channels.
Enenche ya ce “Dole ne idan ka yi gwagwarmaya da makiya, akwai abun da muke kira halayya da dabi’un makiyi.
“Ta wannan fuksa muka kalli harin muka kuma gano cewar su [Boko haram] ne suka kai harin. Duk irin salo ne na yakinsu.
“Bincikenmu ya gano cewa makiyan kasa da ke yankin ne suka kai harin.
“Ina tabbatar wa mutane cewar babu maganar zagon kasa daga sojojin da ke aiki a yanki, don haka su yi watsi da zargin.
“Ina kara tabbatar wa jama’a cewar muna nan kan rantsuwarmu ta yin biyayya ga Hafsan Hafsoshi da Kundin Tsarin Kasa na cewa za mu tsare kasar nan” inji shi.
Enenche ya kuma ce rundunar tsaron a shirye take domin kawo karshen Boko Haram da sauran kalubalen tsaro a fadin kasar nan.