✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abdulmumin Jibrin ya rabu da jam’iyyar APC

Na yi iya yi na a jam'iyyar APC.

Abdulmumin Jibrin, Shugaban Kungiyoyin Yakin Neman Zaben jagoran APC wanda ke neman takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya sanar da shirinsa na ficewa daga jam’iyyar.

Abdulmumin Kofa ya sanar da hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Tsohon dan Majalisar Tarayyar mai wakiltar Kananan Hukumomin Kiru da Bebeji na Jihar Kano, ya ce lokaci ya yi da zai hakura ya kawo karshen zamansa a jam’iyyar APC mai mulki a kasar.

Ya yi alkawarin sanar da sabuwar jam’iyyar da zai koma a ranar Lahadi.

“Na yi wa jam’iyyar APC iyakacin kokarin da zan iya.

“Lokaci ya yi da zan kara gaba na sauya sheka.

“Zan sanar da sabuwar jam’iyyar da zan koma nan da sa’o’i 24 Insha Allah, inda zan bayyana matakin a hukumance,” a cewar sakon da ya wallafa.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ce wasu ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano guda 9 suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.

%d bloggers like this: