Rikicin Jam’iyyar APC ya dauki sabon salo, inda tsoffin daraktocin Kwamitin Gudanarwarta ke zargi Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu da badakalar Naira biliyan uku.
Tsoffin daraktocin da Abdullahi Adamu ya sallama kan zargin almundahanar biliyan N7.5 na zargin shi da yin gaban gansa wajen bude wani asusun sirri tare da ciri Naira biliyan uku daga ciki, duk ba da amincewar Kwamitin Gudanarwar ba.
A sanarwar da suka fitar, korarrun daraktocin sun ce, “Babu kamshin gaskiya kuma an kasa kawo hujja kan zargin almundahana a Sakatariyar Jam’iyyar.
“Tsabar kudi Naira biliyan uku da aka cire daga wannan asusun sirri ba tare da amincewar Kwamitin Gudanarwa mai ci ko Kwamitin Zartarwa ba, duk ba a lokacin muke rike da ofisohinmu aka yi ba.
“Maimakon wannan zargi marar tushe da ake yi, wajibi ne Shugaban Jam’iyya na Kasa ya fito ya yi bayanin wannan saba doka da ka’ida.
“Dole ce ta sa mu fitowa mu yi raddi ga zarge-zarge marasa tushe da yake yi, saboda mu bayyana wa duniya hakikanin lamarin da kuma kafa hujja domin gaba.”
Yadda aka sallame su
A ranar 1 ga watan Afilu, 2022 da Abdullahi ya karbi ragamar APC ne ya kafa kwamitin karbar mulki karkashin tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Ali Sa’ad Birnin Kudu, don nazarin takardun mika mulki da Kwamitin Rikon Jam’iyyar da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jagoranta — da sauran batutuwan da suka shafi jam’iyyar.
Bayan mako uku, a ranar 22 ga watan, bisa shawarar Kwamitin Ali Sa’ad Birnin Kudu, Shugaban Jam’iyyar, ya dakatar da daraktocin sashe-sashe na hedikwatar jam’iyyar sai abin da hali ya yi, saboda zargin almundahana.
Wadanda aka sallama din su ne; Elder Anietie Offong (Walwala); Bartholomew I. Ugwoke (Bincike); Abubakar Suleiman (Kudade); Dokta Suleiman Abubakar (Gudanarwa); Salisu Na’inna Dambatta (Yada Labarai); da Dare Oketade, (Shugaban Sashen Shari’a).
Tuni dai ya mage gurbinsu da sabbin daraktoci.
Aminiya ta gano cewa da farko an bai wa daraktocin hutun dole na wata guda ne, daga ranar 22 ga watan Afrilu zuwa 22 ga watan Mayu, amma bayan nan ba a mayar da su kan kujerunsu ba.
Duk kokarin da suka yi na komawa kan kujerunsu na, ciki har da rubuta wasika ga Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar a ranar 20 ga watan Yuli, bai yi nasara ba.
Daraktoci sun sace N7.5bn —Shugaban APC
A jawabinsa ga manema labarai makon jiya, Abdullahi Adamu ya zargi Kwamitin Riko na Mai Mala Buni da almundahana, yana mai cewa sun bar wa shugabancinsa bashin Naira biliyan 7.5.
Amma a wani martani da daraktoci biyar da ya dakatar tare da shugaban sashen shari’ar suka fitar, sun karyata cewa kwamitin Ali Sa’ad Birnin Kudu ya ba da shawarar dakatar da su.
Don haka suka ce har yanzu su ne halastattun daraktocin jam’iyyar kuma wajibi ne a biya su hakkokinsu kamar yadda aka saba.
A cewarsu, zargin da tsohon Gwamnan Jihar Nasarawan ke yi cewa an bar wa shugabancinsa gadon bashin Naira biliyan 7.5 na shari’o’i ba gaskiya ba ne.
Sun kuma ce, “Mu sanannun jami’a’i ne a Hedikwatar Jam’iyyar APC a lokacin mulkin kwamitin riko.
“Muna kalubalantar (Adamu da duk) mai zargin akwai ma’aikatan bogi, ya fito ya wallafa sunayensu.
“Soki burutsu ne zargin cewa ma’aikata na bin bashin albashinsu a lokacin da shugabanci mai ci ya karbi ragamar jam’iyyar.”
A cewarsu, an biya ma’aikatan jam’iyyar albashinsu har zuwa karshen watan Maris, kafin zuwan shugabancin Sanata Abdullahi Adamu.
“Su ma’aikatan shaida ne, don haka zargin cewa akwa bashin albashi ba gaskiya ba ne,” in ji su.
Suka ci gaba da cewa hutun dole da aka ba su ba shi da asali, kuma an yi ne domin makirci.
“Saboda haka, bisa dogaro da sassan kundin tsarin mulkin APC da dokar aikinta, har yanzu muna daukar kanmu a matsayin halatsattun ma’aikata.
Suka ce, “Muna kalubalantar Shugaban Jam’iyya na Kasa a matsayinsa na gogaggen ma’aikaci ya tabbatar da zargin da yake mana ta hanyar gabatar da rahoton binciken kudin jam’iyyar na 2021.”
A cewarsu, a rohoton “babu ko kalma daya ballanta jimla da ta yi magana a kan biyan kudaden shari’o’i.
“Abin takaici ne zargin da yake yi na an bar mishi bashin Naira biiyan 7.5 na kudaden shari’a.
“Ya kamata a gabatar da jerin shari’o’in da aka yi da za a biya wa wadannan kudaden.”
Adamu ya karyata daraktoci
Mun tunutbi shugaban jam’iyyar na kasa, wanda ya musanta zargin tsoffin daraktocin, yana mai cewa suna da hadama.
“A bin dariya! Sun kasa nutsuwa saboda ganin kudaden da ba a kashe ba, kuma ni ne a kan shugabanci.
“Suna da iyayen gida a wani wuri, ba ma yin kwanmu sai da zakara, kuma ni ba na rara-gefe. Iyayen gidan nasu su fito fili mu buga mana.
“Babu wani abu da na yi gaban kaina a matsayina na Abdullahi Adamu; duk abin da na yi na yi ne da yauwan Kwamitin Gudanarwa na Kasa kuma da goyon bayan mambobnin kwamitin,” in ji shi.
Daga: Sagir Kano Saleh, Isamil Mudasshiru, Saawa Terzungwe