✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abdulaziz Abdulaziz Ya Zama Gwarzon Binciken Kwakwaf

Dan jaridar kafar Media Trust da ya yi binciken kwakwaf kan ayyukan ’yan bindiga har zuwa maboyar Bello Turji ya lashe Kyautar Gwarzon Binciken Kwakwaf…

Abdulaziz Abdulaziz na kafar Trust TV ya lashe Kyautar Gwarzon Dan Jarida Mai Binciken Kwakwaf a talabijin.

Cibiyar Binciken Kwakwaf ta Wole Soyinka ce ta karrama Abdulaziz Abdulaziz, saboda binciken kwakwaf da ya gudanar kan ayyukan ’yan bindiga a Arewacin Najeriya, inda ya je har maboyar gawurtaccen dan ta’adda, Bello Turji, suka tattauna da shi.

Abdulaziz Abdulaziz, wanda shi ne Mataimakin Janar-Edita na Jaridar Daily Trust ya lashe Babbar Kyautar ce bayan rahoton nasa ya yi fintinkau ga ayyukan daukacin ’yan jarida masu binciken kwakwaf da aka zabo domin samun kyautar.

Baya ga shi, ita ma Zainab Bala ta kafar Trust TV, wadda aka gabatar domin samun kyautar ta samu kyakkyawan yawo daga masu shirya taron, kan rahotonta na binciken kwakwaf kan mace-macen mata masu juna biyu a Najeriya.

Su biyun ’yan jarida ne a kafar Rukunin Kamfanin Media Trust, masu kafofin Daily Trust, Aminiya, Trust TV da kuma Trust Radio.

Dan jaridar ya yi fice wajen gudanar binciken kwakwaf domin bankado badakala ba tare da toro ba.

A shekarar 2018, ya lashe Kyautar Gwarzon Dan Jaridar Intanet Mai Binciken Kwakwaf, bayan rahotonsa da ya bankado yadda tsohuwar Ministar Kudi, Kemi Adeosun ke amfani da takardar bogi a matsayin shaidar kammala yi wa kasa hidima (NYSC).

Rahoton nasa ya tayar da kura, har daga bisani Adeosun ta tabbatar da gaskiyar abin da rahoton ya bamkado, sannan ta yi murabus daga mukaminta.

Tun daga lokacin ake kallon Abdulaziz a matsayin matashin da ya bude sabon babi tare da daga darajar aikin jarida na binciken kwakwaf.