✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abdul Amart ya ba Bello Muhammed Bello mota

Bello ya tabbatar da hakan inda sanya hoton Amart a shafinsa na Instagram.

Fitaccen furodusa a Masana’antar Kannywood, Abdul Amart Maikwashewa ya gwangwaje jarumi Bello Muhammed Bello wanda aka fi sani da General a masana’antar da kyautar mota.

Jaruma Maryam Aliyu Obaje, wadda aka fi sani da Madam Korede ce ta bayyana hakan, inda ta ce, “Alhamdulillahi. Ina taya ka murna Bello Muhammed Bello.”

A ranar Juma’a ce Bello din ya sanya hoton Abdul Amart a shafinsa na Instagram a wani rubuce-rubuce da yake yi da ya sanya wa suna ‘mai mutunci challenge’, inda zai sa mutum sannan ya fadi mutuncin da yake da shi.

Da Abdul Amart ya fara, inda ya bayyana cewa ya masa kyaututtuka da dama, ciki har da ba shi motoci da canja wa ’yan biyunsa makaranta da sauransu.

Abdul Amart dai ya sha raba motoci a Kannywood, baya ga sauran kyaututtuka da yake bayarwa.