Fitaccen furodusa a Masana’antar Kannywood, Abdul Amart Maikwashewa ya gwangwaje jarumi Bello Muhammed Bello wanda aka fi sani da General a masana’antar da kyautar mota.
Jaruma Maryam Aliyu Obaje, wadda aka fi sani da Madam Korede ce ta bayyana hakan, inda ta ce, “Alhamdulillahi. Ina taya ka murna Bello Muhammed Bello.”
- Dubun masu yi wa ’yan bindiga safarar man fetur a Sakkwato ta cika
- An ceto hafsan sojin da aka yi garkuwa da shi a NDA
A ranar Juma’a ce Bello din ya sanya hoton Abdul Amart a shafinsa na Instagram a wani rubuce-rubuce da yake yi da ya sanya wa suna ‘mai mutunci challenge’, inda zai sa mutum sannan ya fadi mutuncin da yake da shi.
Da Abdul Amart ya fara, inda ya bayyana cewa ya masa kyaututtuka da dama, ciki har da ba shi motoci da canja wa ’yan biyunsa makaranta da sauransu.
Abdul Amart dai ya sha raba motoci a Kannywood, baya ga sauran kyaututtuka da yake bayarwa.