✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya dauki daliban Kano da suka kammala karatu a Indiya aiki

Sauran ɗaliban kuma, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu don samar musu da ayyuka

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dauki daliban da suka dawo gida bayan kammala karatu a kasar Indiya, wanda gwamnatin jihar ta dauki nauyinsu.

Gwamnan ya sanar da haka ne a lokacin da ya tarbi ɗalibai 150 da gwamnatinsa ta ɗauki nauyinsu don yin karatun digiri na biyu a ƙasar Indiya.

“Ina sanar da cewa za mu ba da aiki kai tsaye ga wadanda suka kammala digirinsu a fannin likitanci da harhada magunguna da injiniya da sauran fannonin kiwon lafiya,” in ji Gwamna Abba a lokacin liyafar da aka shirya musu.

Sauran ɗaliban kuma, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu don samar musu da ayyuka da damar amfani da basirarsu.

Tun da farko Gwamnan da mataimakinsa da manyan jami’an gwamnati  ne suke tarbi daliban a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu da ke Kano, bayan sun kammala karatunsu a Jami’ar Sharda a fannoni daban-daban.

Yayin da yake magana a wajen taron, Gwamna Abba ya bayyana farin cikinsa da alfaharinsa da nasarorin da ɗaliban suka samu. Ya yaba musu kan jajircewarsu, inda ya ce nasararsu, nasarar Jihar Kano ce baki ɗaya.

“Na yi matuƙar farin ciki da ganin waɗannan ɗalibai sun dawo gida da sakamako mai kyau bayan yin karatu a ɗaya daga cikin manyan jami’o’in Indiya. Wannan babbar nasara ce ga Kano da kuma gwamnatina,” in ji gwamnan.

Ya yi kira ga ɗaliban da su zama jakadu nagari na Jihar Kano tare da bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya.

Gwamnan, ya kuma gode wa iyayen ɗaliban kan amincewarsu da gwamnati, tare da yabanwa tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, bisa ƙaddamar da shirin tallafin karatu zuwa ƙetare.

Ya ce mutane da dama, ciki har da wasu daga cikin Kwamishinoninsa, sun ci gajiyar shirin a baya.

An kammala taron ne, inda Gwamna Abba ya bai wa kowane ɗalibi kyautar kuɗi Naira 50,000.

Ga hotunan ɗaliban: