Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tarbi ɗalibai 150 da gwamnatinsa ta ɗauki nauyinsu don yin karatun digiri na biyu a ƙasar Indiya.
Ɗaliban, waɗanda suka yi karatunsu a Jami’ar Sharda, sun dawo gida bayan kammala karatunsu a fannoni daban-daban.
- Bama-baman Lakurawa ne suka kashe mutane a Sakkwato – Sojoji
- Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024
Gwamnan tare da mataimakinsa, jami’an gwamnati, sun tarbi ɗaliban a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu da ke Kano.
Daga bisani, an shirya musu wani taro na musamman a Fadar Gwamnatin Kano don murnar nasarorin da suka samu.
Yayin da yake magana a wajen taron, Gwamna Abba ya bayyana farin cikinsa da alfaharinsa da nasarorin da ɗaliban suka samu.
Ya yaba musu kan jajircewarsu, inda ya ce nasararsu, nasarar Jihar Kano ce baki ɗaya.
“Na yi matuƙar farin ciki da ganin waɗannan ɗalibai sun dawo gida da sakamako mai kyau bayan yin karatu a ɗaya daga cikin manyan jami’o’in Indiya.
“Wannan babbar nasara ce ga Kano da kuma gwamnatina,” in ji gwamnan.
Gwamna Abba ya ce ɗaliban da suka karanci fannin injiniyanci da likitanci za su samu aiki kai-tsaye.
Sauran ɗaliban kuma, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da masu zaman kansu don samar musu da ayyuka da damar amfani da basirarsu.
Ya yi kira ga ɗaliban da su zama jakadu nagari na Jihar Kano tare da bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya.
Gwamnan, ya kuma gode wa iyayen ɗaliban kan amincewarsu da gwamnati, tare da yabanwa tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, bisa ƙaddamar da shirin tallafin karatu zuwa ƙetare.
Ya ce mutane da dama, ciki har da wasu daga cikin Kwamishinoninsa, sun ci gajiyar shirin a baya.
An kammala taron ne, inda Gwamna Abba ya bai wa kowane ɗalibi kyautar kuɗi Naira 50,000.
Ga hotunan ɗaliban: