Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake gabatar da wani ƙwarya-ƙwaryan kasafin kudin bana ranar Talata na naira biliyan 24 a gaban Majalisar Dokokin Jihar Kano don neman amincewarta.
Abba Kabir ya gabatar da rokon ne a cikin wata wasika da shugaban majalisar dokokin jihar, Yusuf Isma’il Falgore ya karanta a zaman majalisar na yau.
- Haɗin-kai shi ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a Zamfara
- Zan dawo da martabar ilimi a Zamfara — Dauda Lawal
Isma’il Falgore ya ce gwamnan ya nemi amincewar majalisar ne kamar yadda sashe na 122 karamin sashe na (A) da (B) na tsarin mulkin 1999 ya tanada.
Ya ce, “kudurin ƙwarya-ƙwaryan kasafin kudin na shekara ta 2023 a karo na byu, ya zama dole saboda wasu dalilai daga ciki har da kudaden da jihar ke sa ran samu daga kwamitin rabon kudade na asusun tarayya da harajin VAT da asusun kula da zaizayar kasa da harajin EMTL da kudaden rance na ayyukan samar da lantarki mai zaman kansa daga Babban Bankin Najeriya da kuma karin kudin shiga na cikin gida”.
Gwamnan ya ce bisa la’akari da wadannan bukatu da kuma muradin aiwatar da wasu muhimman ayyukan raya kasa na gaggawa a cikin jihar, an gabatar da kudirin kasafin kudin a kan bangarorin da suka hadar da biyan kudaden garatuti da naira biliyan hudu.
Kazalika, kudirin da gwamnan ya gabatar ya nuna akwai kuma bukatar kashe naira biliyan 20 a kan manyan ayyuka.
A cewarsa da karin ƙwarya-ƙwaryan kasafin kudin naira biliyan 58 da kuma na naira biliyan 24, kasafin kudin Jihar Kano na shekara ta 2023 a yanzu ya kai naira biliyan 350.
Ana iya tuna cewa, a watan Oktobar da ya gabata ne Gwamna Yusuf ya gabatar da kasafin kudin da ya kai Naira biliyan 350 na shekarar 2024 ta badi, inda a ciki, fannin ilimi ne ya samu kaso mafi tsoka na Naira biliyan 95.