✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya roƙi likitocin Kano su jingine barazanar yajin aiki

Abba ya ce “saɓani tsakanin mutum biyu” bai kamata ya haifar da matsalar jinƙai ba.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya roƙi ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa su dakatar barazanar yajin aikin da suka yi.

Hakan na ƙunshe cikin wani jawabi da Gwamnan ya yi wa haɗakar manema labarai a birnin Dabo a ranar Laraba da daddare.

Gwamnan ya yi gargaɗin cewa hakan zai sanya rayukan al’ummar jihar fiye da miliyan 20 cikin hatsari.

Abba ya tabbatar wa ƙungiyar likitocin cewa kwamitin bincike da ya kafa — kan zargin kwamishinar ayyukan jinƙai ta jihar da cin zarafin wata likita a Asibitin Murtala — ya kammala tattara rahotonsa, kuma yanzu haka rahoton na kan teburinsa, kuma zai ɗauki mataki a kai.

Gwamnan ya kuma bayyana damuwarsa kan matakin ƙungiyar kan abin da ya kira “saɓani tsakanin mutum biyu” bai kamata ya haifar da matsalar jinƙai ba.

Ƙungiyar likitocin dai ta bai wa gwamnan wa’adin sa’o’i 48 ya kori kwamishinar, ko ta tsunduma yajin aiki.

Kungiyar likitocin ta tun a ranar Talata 5 ga watan Nuwamban wa’adin awa 48 na ko dai ya sallami kwamishiniyar ayyukan jinƙai, Amina HOD ko kuma su janye ayyukansu daga Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad a wani mataki na nuna ɓacin ransu kan zargin cin zarafin likitar.

“Kwamishiniyar ba ta cancanci matsayin da aka ba ta ba,” in ji shugaban ƙungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar Kano, Dokta Abdulrahman Aliyu.

Abin da likita ta ce an yi mata

A cikin wani bidiyo da likitar ta fitar ta bayyana cewa, tana aiki tun ƙarfe huɗu na yamma har zuwa ƙarfe 12 na dare a asibitin Murtala, inda take kula da marasa lafiya sama da ɗari biyu.

Likitar ta ce an kawo mata wata yarinya ’yar kimanin shekara biyu wadda take fama da rashin lafiya, inda ta duba yarinyar ta rubuta mata wasu magunguna ciki har da na ciwon mashaƙo da take tunanin yana damun yarinyar.

“A cikin magungunan akwai na mashaƙo, wanda akwai shi a asibitin sai dai yana wani wuri da yake kulle, sun samu guda ɗaya, sai suka riƙa cewa anya na san ma abin da nake kuwa, ganin haka sai na kira wadda take wa marasa lafiya allura na ce ta fara yi masu amfani da waɗanda suka samu,” in ji likitar.

Likitar ta ce bayan ta ci gaba da duba marasa lafiya a daƙin kula da marasa lafiya na gaggawa, “sai kawai wasu mutane suka zo kaina kuma babu kowane jami’in tsaro a tare da ni, sai mutanen suka fara yi mani hayani, daga cikinsu akwai wata mata wai ita kwamishiniya, ta zo tana ta hayaniya tana faɗa, tana buga teburin da nake zaune.

Ni ko ’yar gidan gwamna ce sai an hukunta ni, bayan mutane sun shigo sai na samu dama na kira maigidana da hukumar asibitin, sai dai ban samu wani agaji daga hukumomin asibitin cikin lokaci ba.”

Martanin kwamishinar

A cikin wani bidiyo da ita ma kwamishiniyar jinƙan ta jihar Kano, Hajiya Amina HOD ta fitar ta ce an kira ta a waya ne aka shaida mata cewa wata yarinya na ta suma a asibitin birni na Murtala kuma likita ta ƙi ta duba ta.

Hajiya Amina ta ce bayan ta isa asibitin domin gane ma idon ta sai ta iske likitar zaune ko da ta same ta, ba ta ansa mata sallama ba, “Na ce mata baiwar Allah sannu, ba ta ansa mani ba, sai na sake yi mata magana ba ta ansa ba sai kallona da ta yi a shagiɗe, sai kawai ta tashi daga kan teburin, ta shige cikin wani ɗaki ta buga ƙofa.

Ta kira kwamishinan lafiya da SSG ba su ɗauki waya ba domin ta shaida masu abin da ke faruwa. An rubuta allurar tun safe sun kasa samun ta cikin gari, sun ce a rubuta masu madadinta amman taƙi ta rubuta masu, gashi yarinyar na jin jiki kuma ko gado ba a ba su ba, kuma akwai alluran da yawa a asibitin amman an ɓoye su.” In ji Hajiya Amina.

Kwamishiniyar ta ƙara da cewa mijin likitar ya same ta inda take ya yi mata rashin kunya, inda ya ce “za ku zo ku ci wa matata mutunci na zo na ɗauke ta, an ce ke kwamishina ce, wace ce kwamishina? Waye ma gwamnan ? Bayan haka ma shekara huɗu za ku yi ku sauka.”

Kwamishinar ta ce yaran da ke zagaye da ita sun so tayar da tarzoma saboda kalaman mijin, sai dai ita ce ta taka masu birki.

Hajiya Amina ta ce bayan ta isa gida shugaban jami’an tsaron asibitin ya kira ta ya shaida mata cewa mijin matar ya ɗauke ta, sai shugaban asibitin ne ya ƙarasa duba marasa lafiya.