Gwamna Abba Yusuf ya raba wa mata da matasa 465 da ke tallar kaya a kan titunan Kano tallafin Naira dubu hamsin-hamsin.
Gwamnan ya bayyana cewa manufar rabon tallafin da aka yi ranar Laraba shi ne kara wa masu kananan sana’o’in karfin jari domin dogaro da kansu.
Wadanda suka amfana sun hada da masu sayar da kayan mota da kayan girki da sauransu da ke yawo da kayan a kan tituna inda gwamnan ya yaba musu bisa dagewarsu wajen neman na kansu.
Abba ya bayyana cewa rukuni tara na masu karamanin ne za su amfana da irin tallafin, wanda “kari ne a kan Naira dubu hamsin-hamsin da aka raba wa mata da mata 5,200 domin dogaro da kansu.
- Kotu ta kwace gidajen N11bn a hannun Emefiele
- Uba ya sayar da ’ya’yansa biyar a Sakkwato
- Yadda ake zaman jiran ci gaban Shari’ar Masarautar Kano a kotu
“Shirin ya haifar da kyakkyawan sakamko inda ya kara wa wadanda suka amfana karfin jari.”