Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya a matsayin kwamishina a sabuwar Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida da aka ƙirƙira.
Gwamnan ya bayyana ma’aikatar da kwamishinan zai jagoranta yayin ƙaddamar da ’yan majalisar gudanarwa na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, da Jami’ar Yusuf Maitama Sule da Kwalejin Kimiyya ta Kano.
- Manoma sun dara bayan samun ruwan sama a Taraba
- An saki ɗaya daga cikin jiragen Gwamnatin Nijeriya da aka riƙe a Faransa
Aminiya ta ruwaito cewa, watanni biyar da suka gabata ne Gwamnatin Kano ta ƙirƙiro sabuwar ma’aikatar, amma ba ta sanar da kwamishinan da zai jagorance ta ba sai a yanzu.
Ana iya tuna cewa, Manjo-Janar Idris na cikin jerin sabbin kwamishinonin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa Majalisar Dokokin Kano domin tantancewa.
Manjo-Janar Idris shi ne tsohon Kwamandan Makarantar Horar da Dakarun Soji da ke Kaduna, inda kuma ya riƙe muƙamai daban-daban a tsawon shekaru 30 da ya shafe yana aikin soji.
Bayan ritayarsa daga aikin soji, ya riƙe muƙamin Magatakarda a Jami’ar Baze da ke Abuja.
Manjo-Janar Idris yana da shaidar digiri na biyu har guda biyu daga Jami’ar Tsaro ta Ƙasa da ke Birnin Washington na Amurka.
Haka kuma, ya yi karatu a Cibiyoyin Tsaro a Birtaniya da Pakistan.
Ya karɓi lambar yabo ta zinare a sanadiyyar shafe shekaru 30 yana aikin soji.
A yanzu Manjo-Janar Idris shi ne Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na farko a tarihin Jihar Kano.