Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya kaddamar da wasu kwamitin shari’a biyu da za su binciki yadda aka yi sama da faɗi da dukiyar jihar daga 2015 zuwa 2023, a mulkin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.
A yayin ƙaddamar da kwamitin a ranar Alhamis, Gwamnan ya buƙaci mambobin kwamitin da su yi ƙoƙarin gurfanar da duk wanda suka samu da laifi.
- Gwamnatin Tarayya ta bai wa Rahama Sadau muƙami
- An dakatar da Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa na Kano, Muhuyi Rimin-Gado
Gwamnan, ya ce binciken almubazzaranci da dukiyar al’umma tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a rikicin siyasa a jihar, na daga cikin alkawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.
“Rikicin siyasa na haifar da babban koma baya ga dimokuraɗiyya a duniya. Yana haifar da asarar rayuka da dukiyoyi tare da rashin yarda a tsakanin jama’a da masu mulki.”
“Rikice-rikicen siyasa musamman na 2023 ba za su tafi a banza ba, dole mu hana aukuwar hakan a gaba.
“Kwamitin farko, ƙarƙashin Mai shari’a Zuwaira Yusuf, zai binciki rikice-rikicen siyasa da kuma mutanen da suka ɓace a dalilin rikicin siyasa daga 2015 zuwa 2023.
“Muna sa ran za su bankaɗo waɗanda ke da hannu tare da waɗanda suka ɗauki nauyin aikata rikicin siyasa a 2015, 2019 da kuma 2023.”
Da yake ƙaddamar da kwamiti na biyu, ƙarƙashin jagorancin, Mai shari’a Faruk Lawan, gwamnan ya buƙaci kwamitin ya binciki yadda aka yi almundahana da dukiya da kadarorin jama’ar jihar.
Ya buƙaci kwamitin da kada ya yi ƙasa a gwiwa wajen bankaɗo laifukan da suka shafi almubazzaranci da dukiyar jama’a, musanman a gwamnatin baya.
Sai dai gwamnan ya bayyana cewar matakin ba shi da nasaba da bambanci ra’ayin siyasa ko kuma neman tozarta wani.
Yusuf, ya buƙaci kwamitin biyu da su zage damtse wajen tabbatar da nauyin da ya rataya a wuyansu na yi wa al’ummar Jihar Kano adalci.
Ɗan majalisar tarayya a jami’yyar APC a jihar, Alhassan Ado Doguwa, na daga cikin manyan ’yan siyasa da aka kama lokacin zaɓen 2023, kan zargin kisan kai.
Daga baya kotu ta bayar da belin sa.