Fitaccen Jarumin Kannywood, Sani Musa Danja, ya zama Mai Bai wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Shawara kan Harkokin Matasa da Wasanni.
Sanarwar na cikin sauye-sauyen muƙamai da gwamnan ya yi domin inganta harkar gwamnatinsa.
- A yanke wa ’yan Boko Haram 200 hukuncin kisa da ɗaurin rai-da-rai
- ECOWAS ta shiga taro bayan ficewar Nijar, Mali da B/Faso
Danja, ya yi fice a harkar fina-finain Hausa, kuma ya shiga jerin sabbin masu riƙe muƙamai da shugabannin hukumomi.
Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana jerin sabbin naɗe-naɗen, ciki har da masana daban-daban da aka naɗa domin yin aiki a ɓangarorin lafiya, ilimi, da sauransu.
Ana sa ran Sani Danja zai mayar da hankali wajen bunƙasa harkokin matasa da wasanni a Jihar Kano.
Wannan naɗin ya fara aiki nan take, kamar yadda sanarwar ta bayyana.