Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin gudanar da bincike kan zargin ba da kwangilar samar da magunguna a ƙananan hukumomin jihar 44.
Gwamnan ya kuma ce ba shi da masaniya a kan kwangilar da aka ce kwanan nan aka ba wani Musa Garba Kwankwaso da ake kyautata zaton ɗan uwa ne ga tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Gwamnan ya bayyana haka ne a sanarwar haɗin gwiwa da Kwamishinan Watsa Labarai na Kano, Baba Halilu Dantiye da Daraktan Watsa Labarai na Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa suka fitar.
Wannan sanarwa ta biyo bayan wani bidiyo da fitaccen mai barkwancin nan Bello Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya fitar, inda yake zargin gwamnatin ta Kano da bai wa wani kamfani na Novomed kwangilar sayen magunguna.
A bidiyon, Dan Bello ya yi zargin gwamnatin Kano da bai wa ɗan uwan tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso kwangilar siyan magungunan inda ya ce a duk wata kowace ƙaramar hukuma ta Kano na bayar da naira miliyan tara ga kamfanin na Novomed mallakar Musa Garba Kwankwaso.
Wannan fallasar ta janyo cece-kuce da martani a shafukan sada zumunta na zamani a cikin sa’o’i 24 bayan wallafa bidiyon
Sanarwar ta ce, “Gwamnan ya umarci Shugaban Hukumar Korafe-Korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) da ya gaggauta gudanar da bincike kan wannan zargi tare da bayar da rahoton sakamakon da aka samu don ci gaba da ɗaukar matakin da ya dace.”
Sanarwar ta kara da cewa, Gwamna Yusuf ya kuma buƙaci al’ummar jihar Kano na gari da su ci gaba da haƙuri har zuwa lokacin fitar sakamakon binciken.”