Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da Naira 71,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jihar.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Talata.
- Dattijo ya shiga hannu kan zargin yin luwaɗi da yaro a Zariya
- Lantarki: Za a gina babbar tashar ‘Sola’ a kowace jiha a Arewa
Gwamnan, ya bayyana cewa wannan matakin na daga cikin manufofin gwamnatinsa na inganta rayuwar ma’aikatan jihar.
Ya ce, “Mun amince da Naira 71,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi a Jihar Kano don inganta rayuwar ma’aikata.”
Wannan sabon albashin zai fara aiki daga watan Nuwamba, wanda zai ƙara yawan albashin da gwamnatin ke biya da Naira biliyan shida a matakin jiha da kuma Naira biliyan bakwai a matakin ƙananan hukumomi.
Gwamnan, ya ƙara da cewa ƙarin da aka yi wa malamai 20,737, ya sa an samu ƙarin Naira miliyan 340 a albashinsu.
Ya gode wa kwamitin mafi ƙarancin albashi kan aikin da suka tare sa gabatar masa da rahotonsu, wanda ya kai ga tabbatar da ƙara albashin ma’aikatan jihar.