Matamaikin Kwamishinan ’yan sandan da aka dakatar, DCP Abba kyari, ya shigar da kara a gaban wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja yana kalubalantar tsare shi da gwamnatin kasar ke yi.
A makon da muka yi bankwana da shi ne Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa NDLEA ta tsare Abba Kyari bayan ta bayyana nemansa ruwa a jallo, bisa zargin alaka da safarar miyagun kwayoyi.
- APC ta dage babban taronta na kasa har sai abin da hali ya yi
- Kotu ta yi watsi da karar neman hana Atiku tsayawa takara
A wata sanarwar da Maitamakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a makon jiya, ’yan sanda sun kama DCP Abba Kyari, da wasu jami’an ’yan sanda 4 bisa zarge-zargen samun hannunsu a cin hanci da rashawa.
Aminiya ta ruwaito cewa, Babban Sufeton ’Yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba ne ya ba da umarnin a gaggauta mika Abba Kyarin a hannun Hukumar NDLEA, yana mai umartar NDLEA ta gudanar da bincike kan tuhumar da ake masa.
Sai dai a cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22 da ya shigar, Abba Kyari ya nemi kotun ta tilastawa Hukumar NDLEA ba shi damar hakkinsa na ’yancin dan Adam da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya yi tanadi.
Abba Kyari ya bukaci kotun ta tilasta wa Hukumar NDLEA bayar da belinsa bisa hujjar cewa rashin lafiya da yake fama da tana kara ta’azzara tun bayan da hukumar ta tsare shi.
Sai dai alkalin kotun, Mai shari’a Inyang Ekwo ya ki amincewa da bukatar, inda ya ce karar na kunshe da wasu kura-kurai da ke bukatar martanin gwamnati, lamarin da ya dage sauraron karar zuwa ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu.
Da take zanta wa da manema labarai bayan zaman kotun na ranar Litinin, lauyarsa Cynthia Ikena, ta ce Abba Kyarin yana fama da ciwon suga da hawan jini kuma yana bukatar kulawar gaggawa.