Jagoran Ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa jajircewarsa da jagoranci mai cike da tausayi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar don taya Gwamnan murnar cika shekara 62 a duniya, Kwankwaso ya bayyana Abba a matsayin shugaba abun koyi wanda ya kawo sauyi mai ma’ana a Jihar Kano.
- Gwamnatin Kano ta sanar da ranakun komawa makarantu
- ’Yan bindiga sun kashe sojojin kamaru 6 a kan iyakar Najeriya
Ya ce, “Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nuna ƙwarewarsa tun daga lokacin da yake a matsayin mataimakina, ya yi kwamishina, har zuwa matakin Gwamnan Jihar Kano.
“Cikin ƙasa da watanni 19 kacal, ya sauya akalar Kano ta hanyar aiwatar da shirye-shirye masu yawa a ɓangarori daban-daban na jihar.
“Ina matuƙar farin ciki da tausayi da kulawarsa ga al’umma da kuma jajircewarsa wajen sauraron buƙatunsu da yanke shawarar da ke inganta rayuwar Kanawa.
“A cikin shekaru 62 da ya yi, Gwamna Abba ya kasance mai tasiri a jiharmu, kuma ya gina kansa a matsayin abin koyi wajen gaskiya da jagoranci mai cike da tausayi.
“Allah ya ƙara masa hikima, ƙarfi, da alheri domin ci gaba da yi wa al’ummar Kano hidima. Barka da zagayowar ranar haihuwa, Mai Girma Gwamna.”
An haifi Gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar 5 ga watan Janairu, 1963, ya fito daga Fulanin Sullubawa, waɗanda ke mulkin masarautar Kano.
Abba ya kasance ɗa ga Malam Kabiru Yusuf da Malama Khadijatul-Naja’atu daga Ƙaramar Hukumar Gaya ta Jihar Kano.