Gwamnatin Kano ta sanar da rage wa daliban manyan makarantun jihar kudin makaranta da kashi 50 cikin 100.
Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a daren Litinin.
- Jam’ar gari sun wawushe kayan abincin da gwamnati ta killace
- Yadda shirin sakin madatsar ruwa daga Kamaru ta jefa ’yan Najeriya cikin fargaba
A cewarsa, ya dauki wannan mataki ne bayan ya karbi bakuncin shugabannin makarantun gaba da sakandire mallakin gwamnatin jihar.
“A wannan rana na samu ganawa da dukkanin shugabannin manyan makarantu na gaba da sakandare mallakin Jihar Kano.
“Na ba su umarnin su rage kuɗaɗen da ɗalibai ke biya na makaranta kaso hamsin (50%) cikin ɗari sakamakon yanayin matsi da al’umma suke ciki,” a cewar sanarwar.
Abba Kabir, ya ce ya ba da umarnin rage kudin makarantar nan take.
Hakan dai na nufin daga yanzu daliban Kano da suke karatu a makarantun gaba da sakandire mallakin gwamnatin jihar za su rinka biyan rabin kudin da suke biya ne.