✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba Gida-Gida ya jefa kuri’arsa

An samu hatsaniya a Unguwar Chiranchi inda jami’an ’yan sanda suka bukaci karin ma’aikata.

Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya jefa kuri’arsa yayin da zabe ke gudana a wannan Asabar din.

Abba Gida-Gida ya kada kuri’arsa ce a rumfar zabe mai lamba 033 da ke Makarantar GSS Balarabe Haladu a Unguwar Chiranchi da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa, a maimakon a fara zabe kamar yadda aka tanada, rikici ya mamaye wani yanki na Unguwar Chiranci da ke zaman mazabar dan takarar gwamnan na jam’iyyar NNPP da kuma Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas.

Cikin wani hoton bidiyo da wakilinmu ya nada, jami’an ’yan sanda rike da bindigogi ke ta kai kawo a tsakanin jama’a da ke nuna alamar tsugune ba ta kare ba.

Unguwar Chiranci wadda ke cikin Karamar Hukumar Gwale, tana da tarin rumfunan zabe, inda kuma tun ba yanzu ba an yi hasashen babu lallai a kwashe lafiya saboda tsananin adawa ta siyasa da ke tsakanin jam’iyyar NNPP da kuma APC mai mulki a jihar.

Tuni jami’an ’yan sanda da ke zaman jiran ko ta kwana suka bukaci karin jami’ai yayin da wakilinmu ya hangi wasu matasa suna musayar kutufo a tsakaninsu.

Bayanai dai sun ce ’yar tazara kalilan ce tsakanin rumfunan zabe da jiga-jiga jam’iyyun mabambanta za su kada kuri’arsu.

Sai dai duk da wannan ruguntsumi, an kammala shirin soma aiki zabe a mazabar da ke Sakandaren GSS Balarabe Haladu, inda bayan wani lokaci Abba Gida-Gida ya fita ya kada kuri’arsa.