✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abale: Nas din da ya yi fice da dabanci a Kannywood

Shigowarsa sinima ke da wuya aka fara rububin bin sa aka bar manyan jarumai da suka taru.

A baya sunan Daddy Hikima ya yi fice a masana’antar Kannywood ne a lokacin da yake ta fadi-tsahin neman abin sakawa a bakin salati a rawa daban-daban da yake takawa a masana’antar na tsawon shekaru.

Sunansa na asali Adam Abdullahi Adam, amma yanzu an fi saninsa da suna Abale ko Ojo, saboda rawar da ya taka a fim din ‘A Duniya’ na Tijjani Asase ko kuma shirin ‘Haram’.

Yanayin aikace-aikacen Daddy Hikima a masana’antar a da ya sa ba a san shi ba sosai a baya, kasancewar aikin nasa na cigaban shiri da tsara wajen daukar fim duk ayyuka ne na bayan fage.

Sai dai fitowarsa a fim din na ‘A Duniya’ a matsayin dan daba mara tsoro, ya daga darajarsa, ya kuma sa mutane da dama tunanin ko da ma tun asali shi dan daba ne, suna kuma neman sanin tarihin rayuwarsa.

Dama can masu fitowa a ’yan daba sun sha kokawa a kan yadda sauke ca ana tafiya a masana’antar ana barin su a baya.

A baya an yi manyan masu fitowa a matsayin ’yan daba irinsu Shu’aibu Lawal Kumurci da Tijjani Asase da Auwal Isa West da sauransu, sai kuma yanzu da zamani ne na Abale.

Tarihin Abale a takaice

Yawan fitowarsa a matsayin dan daba ya sa hatta wasu wadanda suka san shi a baya mantawa cewa dan boko ne.

Daddy Hikima wanda haifaffen Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano ne, ya yi karatun boko har zuwa matakin zama nas a Kwalejin Kiwon Lafiya (ta Hygiene) da ke Kano bayan ya yi sakandare a Dawakin Tofa.

Yadda ya fara Kannywood

Daddy Hikima ya dade a yana aiki a masana’antar Kannywood a matsayin mai shirya wajen daukar shiri (Production Manager), ko kuma aikin cigaban shiri da yayi fice a kai, wato Continuity.

Bayan zuwan sinima, sai Daddy ya zama daya daga cikin masu sayar da tikitin shiga kallon fim a sinima da ke Ado Bayero Mall Kano.

Yawanci ba a cika damuwa da shi ba idan ana haska fim, saboda yawancin ana zuwa ne domin ganin manyan jarumai da ke zuwa kallon fim.

Daddy Hikima yana asalin aikinsa na cigaban shiri. (Hoto: Instagram).

Daukakar Daddy Hikima

Duk da cewa cikakken nas ne sannan ya dan samu daukaka a bangaren aikinsa a masana’antar ta Kannywood, an fara sanin sa ne sosai bayan fim din ‘A Duniya’, inda ya fito da sunan Abale.

Fim din ‘A Duniya’ wanda ake nunawa a YouTube, na wani jarumi ne wanda shi ma ya yi fice a matsayin dan daba, Tijjani Asasee ne.

Fim din labari ne a kan wasu abubuwa da ke faruwa a lungu da sakon garuruwa, irinsu ta’addanci da ta’ammali da miyagun kwayoyi da sauransu.

Fim din ya ja hankalin mutane da dama saboda yadda ya taba matsalar da ta shafi rayuwar yawancin mutane kai tsaye.

Duk da cewa a cikin shirin akwai tsofaffi kuma fitattun masu fitowa a ’yan daba, an fi jin sunan Abale, saboda yadda ya taka rawarsa da kyau, da kuma yanayin karfin da ya samu a fim din.

A lokacin da ake haska fim din ‘Ka yi na yi’ na Abubakar Bashir Maishadda, a Karamar Sallar da gabata, Daddy Hikima wanda ya saba sayar da tikitin shiga kallon fim a sinima ya shigo farfajiyar sinimar, amma abin mamaki sai ya zama shi ’yan kalle suke bi, duk da cewa akwai manyan jarumai da suka taru a wurin.

Abubukar Bashir Maishadda ya bayyana mamakinsa kan hakan, inda ya ce, “Allah ke nan! Allah mai yadda Ya so, a lokacin da Ya so.

“A lokacin da muke nuna fina-finanmu na baya, Daddy Hikima tikitin shiga kallon fim yake sayarwa da kuma shigar da mutane sinima, amma yanzu kalli yadda jama’a ke bin sa duuu… har ba masu tsare shi.

“Allah mun gode maKa. Allah Ka kiyaye wannan yaron daga shiga rudun duniya. Ya Allah Ka sa ya ci moriyar lokacinsa. Ya Allah Ka azurta shi ya cigaba da taimakon mahaifiyarsa da ’yan uwansa.”

Daga cikin wadanda suka yi tsokaci a kan sakon na Maishadda akwai Ali Nuhu wanda ya amsa da amin, sai kuma A’isha Aliyu Tsamiya da sauransu.

Daddy Hikima a wasan sallah

Bayan zuwa kallon fim din na ‘Ka yi na yi’ da mutane suka biyo shi, sai Daddy Hikima ya tafi garin Abuja, inda ya gudanar da wasa.

Aminiya ta ga bidiyon wasan, inda mutane cike da gidan wasan suke ta ihu, suna cewa’ “Inda Rabbana’ shi kuma yana cewa ‘ba wahala’ kamar yadda suke fada a fim din ‘A duniya’ tsakaninsu da mai gidansu.

Daddy ya zama jarumi mai tsada?

A yanzu kusan Daddy Hikima ya fara zama jarumin da kusan kowane furodusa yake nema domin ya yi aiki da shi.

A cikin manya-manyan fina-finai masu dogon zango da ake nunawa a YouTube, Izzar So ne kadai ba ya ciki, wanda wasu masu sharhi a kan Kannyood suke ganin shi ma fim din saboda an yi nisa sosai ne.

Amma ko fim din Labarina da ya yi fice sosai, an ga Daddy Hikima ya shigo a cigaban shirin.

Akwai fina-finai irinsu ‘Haram’ da aka dade ana yi, wanda shi ma akwai dabanci a ciki.

Sannan akwai sabon fim din Dauda Kahutu Rarara mai suna Gidan Dambe, wanda Daddy Hikima ne fuskar fim din.

Sai kuma fim din Sanda wanda shi ma yanzu haka ake dauka, wanda shi ne furodusan fim din.