✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘A yi zuzzurfan bincike kan harin da aka kai wa Gwaman Binuwai’

Babban Sufeton ya kuma yi Allah wadai da harin tare da umartar Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar da kara tsaurara matakan tsaro a jihar

Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ba da umarnin a gudanar da zuzzurfan bincike kan harin da aka kai wa Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom.

Kakakin Rundunar ta Kasa, Mista Frank Mba ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

A ranar Asabar  ne dai wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka bude wa tawagar Gwamnan wuta a gonarsa dake kusa da Makurdi babban birnin jihar.

Frank Mba ya ce Babban Sufeton ya kuma yi Allah wadai da harin tare da umartar Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar da ya kara tsaurara matakan tsaro a jihar, musamman a kan Gwamnan.

Ya kuma ce Babban Sufeton ya umarci a gudanar da bincike tare da cewa a kama dukkan wanda yake da hannu a ciki domin ya girbi abinda ya shuka.

Kakakin ya kuma ce saboda a tabbatar ba a bata lokaci a binciken ba, tuni rundunar ta ba da umarnin girke wani ayari daga Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin binciken.

Hakan a cewarsa zai samar da karin taimako ne ga rundunar ta jihar Binuwai, yana mai kira ga mutanen jihar da su kwantar da hankulansu yayin da rundunar ke kokarin lalubo bakin zaren matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.