✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yi wa wanda ya kashe Ummita hukuncin da ya dace – ’Yan China mazauna Kano

Kungiyar ta kuma yin Allah-wadai da kisan

Kungiyar ’yan kasuwa ’yan asalin kasar China mazauna jihar Kano, ta ce tana goyon bayan a yi amfani da doka wajen hukunta wanda ake zargi da kisan matashiyar nan, Ummukulsum Buhari (Ummita) da ake zargin wani dan China da yi.

Kungiyar ta kuma yi Allah-wadai da kisan da ake zargin daya daga cikinsu, Geng Qaunrong, da yi wa Ummitan a Kano.

Kungiyar, karkashin shugabancin Wakilin Mutanen China a Kano, Mista Mike Zhang ce ta fadi haka a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a Kano.

A cikin takardar da Mataimaki na musamman ga Wakilin Mutanen Chinan a Kano, Guang Lei Zhang, ya sanya wa hannu, ta bayyana kisan da aka yi wa matashiyar abin Allah-wadai ne haka kuma laifi ne babba wanda ya kamata kwararru a bangaren jami’an tsaro su tafiyar da shi.

A cewar takardar, mutanen China mazauna jihar Kano suna goyon bayan duk matakin da doka ta tanada wajen tafiyar da lamarin.

Haka kuma, kungiyar ta yaba wa irin tarbar da mutanen China suke samu daga mutanen Kano, inda suka yi fatan dorewar kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu da mutanen jihar.

Haka kuma kungiyar ta lashi takobin ganin ’ya’yanta sun ci gaba da zama masu biyayya ga dokokin Jihar Kano haka kuma masu zaman lafiya tare da taimaka wa wajen ganin Jihar ta ci gaba.

A karshe kungiyar ta mika jajenta ga iyalan marigayiya Ummulkulsum Buhari.

A ranar Jumaar da ta gabata ce al’ummar unguwar Janbulo da ke birnin Kano suka shiga tashn hankali na kisan gillar da aka yi wa matashiya Ummulkusum Buhari inda ake zargi wani dan kasar China da kisanta akan sha’anin soyayya da ke tsakaninsu.