Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarki Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ta umarci al’ummar Muslmin Najeriya su yi Sallar Idi a gida.
A wata sanarwa mai dauke da sa-hannun Babban Sakatarenta, Shaikh Khalid Aliyu Abubakar, kungiyar ta JNI ta ce Kwamitin ta na Fatawa ne ya fitar da wannan fatawa game da Sallar Idin shekarar 2020.
“Kungiyar Jama’atu Nasril Islam…ta kallafa wa Kwamitin Fatawa na JNI, a karkashin jagorancin Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh Alhusainy, yin fatawa game da Sallar Idin 2020 kuma, bayan ya tuntubi [dukkan wadanda suka dace], da kuma lura da halin da ake ciki yanzu na annobar COVID-19 da barazanar da take yi [wa al’umma], ya yanke wadannan shawarwari:
“A dakatar da jam’in Sallar Idul Fidri a wajen garuruwa da birane zuwa wani lokaci.
“Mutum zai iya yin Sallar Idin a gida tare da iyalansa ko ma shi kadai idan ba ya tare da kowa a gidan”, inji snarwar.
- A duba watan Shawwal ranar Juma’a —Sarkin Musulmi
- Annobar COVID-19: Yadda Musulmi zai ribaci 10 ta karshen Ramadan
Ba sai an yi huduba ba
Bayan ta yi bayani a kan yadda za a yi sallar, sanarwar ta ci gaba da cewa an dauke wa mutum huduba idan a gida zai yi.
Sanarwar ta kuma kafa hujja da cewa wannan fatawa ta dogara ne da Hadisin Anas Dan Malik a Sahihul Bukhari, da kuma karantarwar Mazhabar Malikiyya a cikin littafin Mukhtasar.
“Sai dai kuma”, inji sanarwar, “a jihohin da gwamnatoci suka cimma matsaya a kan gudanar da Sallar Idi bisa shawarar kwararru a harkar kiwon lafiya, wajibi ne a bi matakan ba da tazara, da saka kyallen rufe fuska, da amfani da man tsaftace hannu sau da kafa don kare masu ibada”.
Sanarwar ta bukaci malamai su ji tsoron Allah sannan su kiyaye abin da suke fada ko aikatawa don kare muradun addinin Musulunci da al’ummar Musulmi.
Darussan watan Ramadan
Daga nan sanarwar ta yi kira ga Musulmi da su bude zukatansu ga kyawawan darussan da watan Ramadana ke koyarwa sannan su ci gaba da aiki da su har bayan wucewar watan.
Wasu jihohin dai sun ba da damar yin Sallar Juma’a da ta Idi, suna masu cewa za su tabbatar da bin matakan kariya daga kamuwa da coronavirus.
Sai dai a wasu jihohin kamar Kano, ra’ayi ya bambanta, inda Majalisar Malamai ta ce gwamnatin ba ta zurfafa tunani ba kafin ta yanke hukunci.