Kyawawan dabi’un Ma’aiki (SAW) suka fi dacewa a yi koyi da su wajen tunawa da ranar haihuwarsa.
Ranar Litinin ce a watan Rabi’ul Awwal, malaman tarihi suka tafi a kan cewa ita ce aka haifi Annabi Muhammad (SAW) duk duk da cewa akwai sabani a kan nawa ga wata ne amma wadansu sun tafi a kan 12 ga watan ne.
Koma dai yaya abin yake al’ummar Musulmi a fadin kasar nan suna raya watan da karatun Alkur’ani da Ishiriniya,da diwani da majalisin ambato da tarihinsa (SAW) a gidaje da majalisu da Islamiyoyi da sauransu.
Amma me ya kamata a matsayinmu na masoya Annabi Muhammad (SAW) mu yi koyi da shi a irin wannan lokaci?
Wani Malami mai hikima ya fadi a cikin harshen Larabci cewa “In son ka gaskiya ne, shi mai so ga wanda yake so mai yin biyayya ne”.
Ke nan me ya kamata mu siffantu da su a wannan ranaku da muke bukukuwan tunawa da fiyayyen halitta da suka fi karantarwar Alkur’ani da hadisansa?
An tambayi Sayyida A’isha (Allah Ya kara mata yarda) a kan halayen Manzon Allah (SAW) sai ta ce “ Halayensa su ne Alkur’ani.” Ke nan in za mu kiyaye karantarwar Alkur’ani tare da aiki da shi za mu siffantu da shi (SAW).
Haka in muka koma wajen siffofinsa kamar yadda malaman tarihi suka hakaito mutum ne mai tarin gemu sannan ba ya barin gashin baki kuma ba ya kwal kwabo ko kwalkwal amma yana yin saisaye, ken an ba ya tara suma da yawa.
A bangaren halaye kuma bayan la’akari da karantarwar Kur’ani sai mu dubi yadda ya yi rayuwarsa da sahabbai da irin gwagwarmayar da ya sha a fagen yaki da zamantakewarsa da wadanda ba Musulmi ba.
Manya daga cikin kyawawan halayen sa sun hada da;
Annabi (SAW) mutum ne mai amana in da za mu duba yadda Sayyida Khadija ta mallaka masa dukiyarta don ya rika yi mata fatauci kuma Allah Ya sanya albarka a ciki, ta kai har makiyansa (SAW) suna kiransa da amintacce.
Hali na biyu abin koyi shi ne, Annabi Muhammad (SAW) mutum ne mai hakuri kwarai da gaske.
Na uku mutum ne wanda yake da saukin sha’ani wajen tafiyar da iyalansa.
Sannan mutum ne mai kyauta matuka wanda har ta kai ba ya tara dukiya, da ta shigo zai raba wa mabukata.
A wannan dan karamin fili ba zan iya fadin ko kashi daya cikin dari na kyawawan halayensa (SAW) ba, amma yana da matukar muhimmanci mu koma ga malaman tarihi mu san su sannan mu yi koyi da su.
A baya-bayan nan an samu wadansu masu kokarin ganin sun habaka wannan biki ta hanyar yin gangami da suka hada da Islamiyoyyi da Zawiyoyi da Sha’irai da sauran da’irori masu hidima don Manzon Allah (SAW), suna zagaya wasu daga cikin manyan tituna a wasu jihohin Arewa suna rera wakokin yabonsa (SAW) da sauransu inda abin yana kayatarwa matuka ta yadda manya da kanana maza da mata suke yin ado suna nuna murnarsu.
Sai dai wani kalubale shi ne yadda wadansu matasa batagari kan yi amfani da wannan dama su yi shiga wadda ba ta dace ba. Wadansu da makamai, wadansu ma har shaye-shaye suke yi inda za ka ga ana samun fadace-fadace wanda hakan ya saba wa karantarwarsa (SAW), domin shi Musulunci addini ne na zaman lafiya.
Daga karshe ina yi wa daukacin Musulmin duniya murna da samuwarsa (SAW) kuma da zuwansa ne addinin Musulunci ya cika.
Sannan ina kira mu yi koyi da kyawawan halayensa a yayin bikin don samun lagwadar da Allah Ya tanadar sakamakon son da muke yi masa (SAW).
Sanusi Hashim Abban Sultana, Mai sharhi ne a kan al’amuran yau da kullum, ya rubuto ne daga Jihar Katsina. 08065507271