Mai Alfarma sakin Musulmi Muhamad Sa’ad Abubakar ya bukaci al’ummar Musulmi a Najeriya da su kara neman kusanci da Allah da kuma yawaita addu’o’i.
Sarkin Musulmi ya yi kiran ne yayin ayyana Juma’a 21 ga watan Agustan 2020, a matsayin ranar 1 ga watan Muharram na Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1442 Bayan Hijira.
Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya NSCIA, ta bayyana haka a ranar Alhamis ta bakin Mataimakin Babban Sakatarenta, Farfesa Salihu Shehu.
Ya ce babu tabbacin ganin watan Muharam a duban farko da aka yi ranar Laraba, wadda ita ce 29 ga watan Zhul Hajji, 1441 Bayan Hijira.
“Saboda haka, Shugaban NSCIA, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya amince da ranar Juma’a 21 ga Agusta, 2020 a mats—ayin ranar 1 ga Muharram, 1442 Hijiriyya.
“Majalisar na kira ga al’ummar Musulmin Najeriya da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin dukkan ‘yan kasa.
Sarin Musulmin ya kuma yai wa Musulmi fatar za a shiga sabuwar shekarar lafiya, tare da kiran su da su kara dagewa wajen ibada da addu’o’in neman Allah Ya kawo karshen annobar coronavirus.