✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A watanni shida na farkon mulkina zan sauya fasalin Najeriya —Atiku

Ana gama rantsar da ni zan fara aiwatar da ayyukan raya kasa ta hanyar sake fasalin Najeriya.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya tabbatar da cewa watanni shida kacal sun isa ya sauya fasalin Najeriya da zarar ya kafa gwamnati.

Ya ce daga lokacin da aka gama rantsar da shi zai fara aiwatar da ayyukan raya kasa ta hanyar sake fasalin Najeriya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito tsohon Mataimakin Shugaban Kasar na wannan furuci yayin yakin neman zabensa ga ’yan Najeriya mazauna ketare a Abuja.

Atiku wanda tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na Kasa, Dokta Okwesilieze Nwodo ya wakilta, ya ce sun kammala duk wasu shirye-shirye na cimma muradin sauya fasalin kasar da zarar akalar jagoranci ta dawo hannunsu.

A cewarsa, Najeriya za ta dawo kan turba madaidaiciya muddin ya zamana an danka wa kowanne yanki akalar jibintar albarkatun da yake da su.

Wazirin Adamawa ya ce tsare-tsaren bunkasa harkokin zamantakewa da tattalin arzikin da tun a yanzu ya tanada za su kai kasar zuwa ga ci.

Ya ce zai yi amfani da ajandar sa ta sauya fasalin Najeriya domin ya kawo karshen matsalar tsaro da sauran kalubalen da kasar nan ke fama da fuskanta.

Ya sake jaddada cewa Najeriya na bukatar sabon jagoranci na gari wanda zai sharewa kasar hawayen ta wajen fuskantar matsalolin da suka addabe ta da kuma cirewa kasar kitse a wuta.

Atiku ya bayyana manyan kudirorin da ya ce gwamnatinsa za ta sanya a gaba da suka hada da hada kan kasa da samar da tsaro da ilimi da tattalin arziki da kuma tabbatar da mulkin tarayya