Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Jigawa (JISIEC) ta sanya ranar Asabar 26, ga watan Yunin Shekarar 2021 a matsayin ranar da zata gudanar da zabuka a Kananan Hukumomi 27 dake Jihar.
Shugaban hukumar, Alhaji Adamu Ibrahim Roni ne ya bayyana hakan Yayin da yake gabatrtwa da wakilan jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki kan harkokin zabe jadawalin zaben a shalkwatar hukumar dake Dutse a ranar Litinin
- Abubuwa 14 da ya kamata ku sani kan tsohon shugaban Chadi, Idriss Deby
- Daliban Jami’ar Jos 2 sun mutu a rikicin matsafa
- Gobara ta lakume ofishin INEC a Kano
Ya ce za a fara siyar da fom din fitar da ’yan takara na shugabancin Karamar Hukumar da na Kansiloli daga ranar 12 zuwa 21 ga watan Mayun 2021.
Kazalika, shugaban ya ce kamar yadda yake a cikin kundin zabe da aka ba jam’iyyun siyasa, za a gabatarwa hukumar fama-faman ’yan takara da sunayen wakilan jam’iyya da za su tsaya a kan Akwatin zabe da sunayen ’yan takarar da aka fitar daga ranar 13 zuwa 27 na Mayun 2021.
Alhaji Adamu Roni ya kuma ce jam’iyyun siyasa ne ke da alhakin daukar nauyin tantance ’yan takarr da za su fafata da takwarorinsu, wanda ake sa ran gudanarwa tsakanin ranakun 23 da 27 ga watan Mayun 2021.
Shugaban ya ce hukumar ce kadai ke da alhakin sanar da lokacin farawa da kammala zaben, inda ya ce kuma jami’anta ne kadai ke da alhakin rarraba kayan zaben a ko’ina a fadin Jihar.