✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A watan gobe Super Eagles za ta kara da Bafana-Bafana a Afirka ta Kudu

Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta tattabatar da gayyatar da kasar Afirka ta Kudu ta yi mata don yin wasan sada zumunci…

Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta tattabatar da gayyatar da kasar Afirka ta Kudu ta yi mata don yin wasan sada zumunci a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles da kuma Bafana-Bafana ta Afirkat ta Kudu a ranar 14 ga watan gobe.
Bayanin haka na kunshe ne a wata takardar da  Mataimakin Daraktan hulda da ’yan jaridu na Hukumar, Mista Ademola Olajire ya rabawa kafofin watsa labarai a ranar Litinin da ta wuce.
Bayanin ya nuna Najeriya za ta yi amfani da zaratan ’yan kwallon Super Eagles ne a lokacin wasan kamar yadda ita ma Afirka ta Kudu ake sa ran za ta yi amfani da nata zaratan don wasan ya kayatar.
Hukumar ta kara da cewa a duk shekara Afirka ta Kudu na shirya wasan sada zumunta ne don karrama dan gwagwarmaya Nelson Mandela kuma wasan zai gudana ne a filin wasa na Moses Mabhida da ke Durban.
Takatar ta kalato cewa shugaban hukumuar kula da wasanni ta kasa NFF, Alhaji Aminu Maigari ya tabbatar da wannan labari.  “Mun sanya hannu a yarjejeniyar da muka kulla a tsakaninmu da kasar Afirka ta Kudu don yin wasan sada zumunta a ranar 14 ga watan Agusta don karrama Nelson Mandela kuma mun yi farin ciki da aka yi mana wannan gayyata”.
“Najeriya za ta gabatar da zaratan ’yan kwallonta wadanda suka yi fice ne a lokacin wasan kamar yadda ake sa ran Afirka ta Kudu za ta yi amfani da nata zaratan.
Filin wasa na Moses Mabhida shi ne filin da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta yi kaca-kaca da kasar Mali da ci 4-1 a wasan kusa da na karshe (Semi-Fainal) a gasar cin kofin Afirka da ya gudana a farkon shekarar nan da muke ciki.
Shi ma shugaban Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta Afirka ta Kudu (SAFA) Kirsten Nematandani an ji yana fadin: “ Muna farin cikin shirya wannan wasa na sada zumunci don karrama tsohon shugaban kasa Mista Nelson Mandela a tsakanin Afirka ta Kudu da Najeriya”.