Akalla mutum 323 ne aka kashe cikin wata uku a fadin Jihar Kaduna.
Gwamnatin Jihar ta ce an yi garkuwa da kimanin mutum 949 daga watannin Janairu zuwa Maris na 2021.
- Babu ranar dawowar albashin N30,000 a Kano
- Za a biya ’yan fansho karin kudi a watan Mayu
- COVID-19: NAFDAC ta amince da rigakafin Pfizer
Kwamishan Tsaron Harkokin Cikin Gidan Jihar, Samuel Aruwan ya shaida wa taron zangon farkon 2021 kan sha’anin tsaro cewa jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 64 yayin artabu a fadin Jihar.
Ya ce Mazabar Kaduna ta Tsakiya ita ce ke da mafi yawan mutanen da abun ya shafa idan an kwatanta da sauran gundumomin da ke Jihar.
“A cikin mutane 323 da aka kashe, maza 292 ne, mata 20, sai kananan yara 11.
“Mutum 236 da aka yi wa kisan gillar an yi musu ne a Kananan Hukumomin Birnin Gwari, Chikun, Igabi, Giwa, da Kajuru.
“An kashe mutum 77 Birnin Gwari, Chikun mutum 52, Igabi 45, Giwa 42, sai Kajuru mutum 20, duk a wata ukun farkon wannan shekarar.
“A Mazabar Kudancin Kaduna kuma an kashe mutane 68; wadanda biyar daga cikinsu mata ne ’yan kasa da shekaru 18.
“A Karamar Hukumar Kajuru na kashe mutum 28, Zangon Kataf mutum 14, Kagarko 12.
“Arewacin Kaduna shi ne mafi karanci wurin yawan mutanen da aka kashe —mutane 19, inda Zariya ke da kaso mafi yawa na mutum shida da abun ya ritsa da su a yankin,” a cewarsa.