Kawo yanzu, jimillar bashin da gwamnatin Tinubu ta karbo daga Bankin Dunia a cikin wata hudu ya kai Dala biliyan 2.15, wato kimanin Naira tiriliyan 1.6.
Hakan na zuwa ne bayan — a karo na uku cikin wata hudu — Shugaba Tinubu ya ciyo karin bashin Naira biliyan 536 (Dala miliyan 700) daga Bankin da nufin bunkasa bangaren ilimin ’yan mata da kuma ba su tallafi a Najeriya.
- NAJERIYA A YAU: “Yadda Na Sayar Da Kayan Gadona Na Yi Karatu”
- A gaggauta kuɓutar da sauran ɗaliban jami’ar da aka sace a Gusau — Tinubu
“Bankin Duniya ya amince ya kara wa Najeriya bashin Dala miliyan 700 domin Bunkasa Ilimin ’yan mata da ba da tallafi, wanda zai mayar da hankali kan ilimin sakandare a wasu jihohi.
“Karin rancen zai bunkasa ayyukan da aka eyi a wasu jihohi bakwai zuwa 11 domin kara yawan wadanda za su amfana, ciki har da yan matan da ba sa zuwa makaranta, wadanda aka aurar da kuma nakasassu,” in ji sanarwar Bankin Duniyar.
Karo na uku ke nan a cikin wata hudu da Gwamnatin Tinubu ta samu bashin Bankin Duniya tun bayan hawan Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.
Kawo yanzu, jimillar bashin da gwamnatin Tinubu ta karbo a cikin wata hudu ya kai Dala biliyan 2.15, wato kimanin Naira tiriliyan 1.6.
Da farko Tinubu ya ciwo bashin Dala miliyan 750 domin bunkasa bangaren wutar lantarki,
A karo na biyu ya samu rancen Naira biliyan 383 (Dala miliyan 500) domin tallafa wa mata.
Sai kuma bashin Naira biliyan 536 (Dala miliyan 700) da ya ciyo a yanzu na bunkasa ilimin ’yan mata da kuma ba su tallafi.
Ofishin Kula da Basuka na Najeriya (DM), ya sanar cewa zuwa karshen watan Yuni, yawan bashin da Bankin Duniya ke bin Najeriya ya kai Dala biliyan 14.5, kimanin Naira tiriliyan 11.
A ganinku wane irin tasiri basukan da ake karbowa daga Bankin Duniya da sauran hukumomin duniya za su yi ga ’yan Najeriya?
Wace hanya ya kamata a bi domin hana karkatar da kudaden?