✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice..A wasannin mako

Mutum 15 sun mutu a yamutsin filin kwallo a Kongo Akalla mutum 15 ne aka ruwaito sun mutu a wani yamutsi da ya rutsa da…

Mutum 15 sun mutu a yamutsin filin kwallo a Kongo

Akalla mutum 15 ne aka ruwaito sun mutu a wani yamutsi da ya rutsa da ’yan kallo a filin wasa na Kongo (DR Congo) a karshen makon jiya.
Al’amarin ya faru ne a garin Kinshasa bayan da jami’an tsaro na ’yan sanda suka harba barkonon tsohuwa a lokacin da fada ya kaure a tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa biyu a wani wasan karshe.
Rahoton ya ce magoya bayan kulob din da ke Kinshasha sun harzuka ne bayan da wani kulob da ya fito daga yankin Gabashin kasar ya doke nasu da ci daya mai ban haushi da hakan ta sa suka farwa wasu jami’an tsaro su kimanin hudu, su kuma da suka ga haka sai suka rika harba barkonon tsohuwa al’amarin da ya sa jama’a suka ranta cikin na kare da hakan ta sa wasu suka fadi aka tattake kuma aka yi asarar rayuka akalla 15.
Minista mai kula da yankin, Eammnuel Akweti ya tabbatar da aukuwar lamarin.
“Magoya bayan sun kai wa hudu daga cikin jami’an tsaro hari ne inda su kuma suka rika harba barkonon tsohuwa da hakan ta sa ya janyo asarar rayukan akalla mutum 15 a yamutsin”, inji shi a lokacin da yake hira da manema labarai.
Ministan ya ce wadanda suka mutu ana kyautata zaton sun mutu sakamakon shakar iskar barkonon tsohuwa da suka yi  yayin da wasu 24 kuma suka samu munanan raunuka inda aka garzaya da su asibiti  don yi musu magani
Sai dai wani jami’in tsaro da bai so a ambaci sunansa ba ya ce akalla mutane 18 ne suka mutu a yamutsin. Tuni jami’an tsaro suka fara bincike don gano musabbabin rikicin.

Dabid Luis zai koma FC Barcelona

dan kwallon baya a kulob din Chelsea da ke Ingila Dabid Luis ya fara shirin komawa kulob din FC Barcelona da ke Sifren da zarar an fara kakar wasa mai zuwa.
Rahotanni sun ce tuni kulob din Chelsea da na Barcelona suka kulla yarjejeniyar cinin dan kwallon a kan Fam miliyan 32. Ana sa ran Dabid Luis zai rika karbar albashin Fam dubu 100 a duk mako a kulob din na Barcelona.
Da zarar an kammala gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a wata mai zuwa ne ake sa ran Luis zai rattaba wa yarjejeniyar hannu.

An sanya kulob din Aston billa a kasuwa

Mai kulob din Aston billa da ke Ingila Mista Randy Lerner ya bayar da sanarwar sanya kulob din a kasuwa.  Ya ce tuni ya yi wa kulob din farashin Fam miliyan 200 ga duk mai bukata.
A gasar Premier ta Ingila a bana, kulob din ya gama a matsayi na 15 ne daga cikin kungiyoyi 20 da suka fafata a gasar. Kenan kulob din zai cigaba da zama a gasar a kakar wasa mai zuwa tun da ya haye matakin koma baya (relegation).

Sukotlan ta bayyana ’yan kwallon da za su fafata da Najeriya a wasan sada zumunta

kasar Sukotlan ta bayyana sunayen ’yan kwallon da za su fafata da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a wasan sada zumunta da za a yi a ranar 28 ga watan nan da muke ciki.
Za a gudanar da wasan ne a filin wasa na kulob din Fulham da ke Ingila da ake wa lakabi da Caben Cottage.
Wasan sada zumuntar zai zama gwajin dafi ne ga kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a shirye-shiryen tafiya gasar cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a  wata mai zuwa.