Kulob din Swansea ya kori kocinsa
Kulob din Swansea City da ke wasa a gasar rukunin Premier na Ingila ya bayar da sanarwar sallamar kocinsa Micheal Laudrup a ranar Talatar da ta wuce.
Kulob din ya shiga matsala ne bayan ya samu nasara a wasa daya kacal daga cikin wasanni da hakan ta sa yake gab da fadawa tarkon sahun koma-baya (relegation) a gasar ta Premier.
A ranar Asabar da ta wuce ne kulob din West Ham United ya lallasa na Swansea da ci 2-0 a gasar rukunin Premier ta Ingila da hakan ta sa kulob din yanke shawarar raba-gari da kocinsa.
Joseph Yobo ya koma kulob din Norwich City
Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles da ke buga kwallo a kulob din Fenerbahce da ke Turkiyya Joseph Yobo ya canza sheka zuwa kulob din Norwich City da ke Ingila a matsayin aro a karshen makon jiya.
Wata sanarwa da kulob din Fenerbahce ya fitar ta nuna tuni kulob din ya amince da tura Yobo kulob din Norwich City a matsayin aro zuwa karshen kakar wasa ta bana.
“Kulob din Fenerbahce na godiya ga Joseph Yobo a kan gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake mana wasa, kuma mun amince ya koma Ingila ne don cigaba da wasa a kulob din Norwich City daga nan zuwa karshen kakar wasa ta bana”, inji sanarwar.
Yobo ya shafe shekara goma a kulob din Eberton da ke Ingila. Ya buga wa kulob din wasa har sau 258 a tsakanin shekarar 2002 zuwa 2012 kafin ya canza sheka zuwa Turkiyya.
Nsofor zai samu albashin Naira miliyan 66 a Italiya
Shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagles Obinna Nsofor zai samu albashin Yuro dubu 300 kwatankwacin Naira miliyan 66 a tsawon wata shida da zai shafe a kulob din Cheibo da ke Italiya, kamar yadda kafar sadarwar labarin wasanni ta MTNfootball ta sanar a ranar Litinin da ta wuce.
Nsofor wanda yake buga wa kulob din Lokomotib Moscow da ke Rasha wasa ya samu damar komawa Italiya ne bayan kulob din ya bayar da shi a matsayin aro na tsawon wata biyar watau zuwa karshen kakar wasa ta bana.
A tsawon watanni biyar da zai kwashe ne aka yi yarjejeniyar za a ba shi albashin Yuro dubu 300.
Tun bayan da Nsofor ya koma Rasha a shekarar 2011 yake cin benchi da hakan ta sa kulob din yanke shawarar bayar da shi ga wani kulob a matsayin aro.
Ya koma kulob din Cheibo na Italiya ne wanda yake tangal-tangal a gasar rukunin Italiya inda yanzu haka kulob din ke matsayi na 16 daga cikin kungiyoyi 20 da ke fafatawa a gasar Serie A ta kasar.
dan kimanin shekara 26, Nsofor ya taba buga kwallo a kulob din Chiebo kimanin shekara biyar da suka wuce kuma ya zura kwallaye 20 daga cikin wasannin 86 da ya yi wa kulob din a wancan lokaci.