✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A soma duban watan Safar — Sarkin Musulmi

Watan Safar shi ne na biyu a jerin watanni 12 na kalandar musulunci.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya umarci al’ummar musulmi da su fara duban watan Safar na shekarar 1446 Hijiriyya daga gobe Lahadi.

A gobe Lahadi ce dai watan Muharram — wato na farko a kalandar musulunci zai cika kwanaki 29 da kamawa, daidai da 4 ga watan Agusta na shekarar 2024 ta Miladiya.

A madadin Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Masarautar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid, ne ya fitar da sanarwar.

Farfesa Sambo, ya ce duk wanda ya samu ganin watan ya sanar da Majalisar Sarkin Musulmi ko wani uban kasa ko hakimi domin sanar da al’umma.

Watan Safar shi ne na biyu a jerin watanni 12 na kalandar musulunci.

Ya roki Allah Ya taimake su ga aikin addini da suke yi.