✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A shirye nake in sa hannu a hukuncin kisa kan makashin Hanifa – Ganduje

Ya c ce ba zai yi wata-wata ba muddin kotu ta yanke hukuncin.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce a shirye yake ya sa hannu a aiwatar da hukuncin kisa a kan wanda ake zargi da kisan Hanifa muddin kotu ta yanke masa hukuncin.

Tuni dai wanda ake zargin mai suna Abdulmalik Tanko ya amsa aikata laifin da ake masa na sacewa tare da kisan dalibar mai shekara biyar.

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, inda ya ce ba zai yi wata-wata ba wajen sanya hannu a zartar masa da hukuncin.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin, lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnati da ta Majalisar Dokokin Jihar zuwa gidan su Hanifa da ke unguwar Dakata/Kawaji a birnin Kano.

Ganduje ya ce, “Muna da tabbaci daga kotun da ta fara sauraron shari’ar cewa za a yi adalci.

“Babu wanda za a bari ya ci banza. Duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan mummunan laifin shi ma za a kashe shi ba tare da wani bata lokaci ba. Mu a gwamnatance har ma mun fara yunkurin hakan,” inji shi.

Mutane da dama daga ciki da wajen Jihar Kano dai na ci gaba da kiran lallai a hukunta wanda ake zargi da kisan yarinyar.

Daga cikin wadanda suke goyon bayan a hukunta shin har da uwar gidan Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Buhari.

%d bloggers like this: