Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi kasashen duniya kan su zage damtse wajen daukar darasi daga annobar COVID-19 domin tunkarar wasu da za su zo a nan gaba.
Babban Magatakardar majalisar, Antonio Guterres shine ya yi gargadin a sakon shi na bikin Ranar Shirin Yaki da Annoba ta duniya karo na farko da ya gudana ranar Lahadi.
- #EndSARS: MDD ta ja kunnen Najeriya kan kashe masu zanga-zanga
- Tallafin Korona: Trump ya rattaba hannu kan kudirin raba wa Amurkawa Dala tiriliyan 2.3
Antonio ya ce, “Bikin wannan ranar karo na farko ya zo ne karshen shekarar da ta zo wa duniya da ba-zata da kuma jefa ta cikin rudani.
“Yayin da muke kokarin farfado wa daga wannan annobar da muke ciki, ya zama wajibi mu fara tunani a kan wata da za ta iya sake bulla a nan gaba,” a sakon na Babban Magatakardar.
Ya kuma yi kira wajen ganin an kara bunkasa harkokin lafiya da kuma fito tsare-tsaren tallafa wa wadanda ke sahun gaba wajen yaki da annonbar da kuma bukatar hada karfi da karfe don yin aiki tare tsakanin kasashe.
“A cikin wannan fadi-tashin da muke yi, dole ne kimiyya da fasaha su zame mana jagora. Hadin kai da kuma aiki tare tsakanin kasashe shima wani ginshiki ne; babu wanda zai zauna lafiya har sai dukkan mu muna da lafiya,” inji shi.
Mista Antonio ya kuma jinjina wa ma’aikatan lafiya da ma sauran mutane masu ayyuka na musamman da suka sadaukar da rayuwar su wajen yaki da annobar.
“A kokakin mu na murmurewa daga wannan annobar, ya kamata mu habbaka hanyoyin kariya daga gareta saboda mu shirya wa wacce za ta zo a nan gaba,” inji Abtonio.