✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rika kyautata zato ga masu harkar waka da fim – Gimbiyar Mawaka

Mawakiya A’ishatu Haruna Bauchi, ta fito ne daga Unguwar Falaliyawa da ke garin Liman Katagum a karamar Hukumar Bauchi a Jihar Bauchi. Mawakiyar wadda aka…

Mawakiya A’ishatu Haruna Bauchi, ta fito ne daga Unguwar Falaliyawa da ke garin Liman Katagum a karamar Hukumar Bauchi a Jihar Bauchi. Mawakiyar wadda aka fi sani da Gimbiyar Mawakan Bauchi, ta ce ta rika yin wakoki a boye saboda gudun matsi daga danginta kafin Allah Ya sa ta fara fice, kuma ta bayyana wa Aminiya abin da ya ba ta sha’awar shiga harkar waka da irin kalubalen da ta fuskanta:

 

Me ya ba ki sha’awa kika fada harkar wakoki?

To, Alhamdulillah, abin da ya ba ni sha’awa shi ne tun ina yarinya ina makarantar Islamiyya na fara sha’awar wakoki. Sai kuma wasu shekaru da suka kai 18 zuwa 20 da suka gabata, na so shiga harkar fina-finai, amma ban samu goyon baya ba a gidanmu. Ana nan bayan na fita daga gidan mijina, sai zuciyata ta raya min cewa in tunkari abin da nake so din nan, tare da yarda cewa Allah zai taimaka min, ta yiwu hakan ya zamo hanyar cin abincina. Sai kawai na tsinci kaina a masana’antar fina-finai ina fitowa jifa-jifa ina kuma yin waka. 

To kamar yadda na gaya maka ina karama ina makarantar Islamiyya, ni ce daliba ta farko ko ta biyu da in aka zo lokacin Mauludi ake koya mana yadda za mu rika yin kasidu. Kuma da ka ake koya mana kasidun don rerawa a filin Mauludi na makarantarmu ko inda aka gayyace mu a wasu makarantu.

Kin ce kin so ki shiga harkar fim amma aka hana ki, da kika shiga daga baya kin yi kamar fim nawa?

Na fara waka a gida, amma ganin a baya an hana ni, ban nuna musu ga abin da nake yi ba. Tunda a lokacin ba ni da aure, wani lokaci in zan fita unguwa sai in shiga sutudiyo in yi wakar a cikin sirri. To da abubuwa suka fara fitowa fili, sai na ce ya kamata in sanar a gida halin da ake ciki don kada su tsangwame ni, kuma na nemi su ba ni goyon baya, kuma su yi min addu’ar Allah Ya sa wannan abin da nake yi ya zame min alheri. Alhamdulillahi na samu goyon bayan mahaifiyata da ’yan uwana ta bangarenta da na mahaifina.

Kina da wakoki kamar guda nawa a yanzu?

Na rera wakoki a bangaren siyasa da sarauta da na bukukuwa. Kuma akwai kasidun da na yi album a kan yabon Annabi (SAW) da nake sa ran za su fito nan da watan Mauludin bana.

Wace waka ce ta fi fito da ke a tsakanin jama’a?

Gaskiya an fi sanina da wakokin siyasa. Wakokin da na yi suna da yawa amma akalla akwai fitattu guda goma ko fin haka. Akwai wasu hudu kan zaman lafiya da zamantakewar iyaye da ’ya’ya da sana’o’i da sauransu wadanda na yi da hadin gwiwar wasu manyan kungiyoyi na kasar nan tare da amincewar gwamnatin Jihar Bauchi. Idan Allah Ya yarda za kaddamar da su nan gaba kadan.

Wace waka ce kika yi aka yi miki kyautar da ba za ki mance ba?

Alhamdulillahi, akwai wakar da na yi a Kwantagora ta Jihar Neja, inda a karo na farko aka ba ni kyautar mota kirar Golf. Na biyu akwai wakar da na yi wa Mai girma Gwamna Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar, shi ma ya ba ni kyautar mota. 

Sannan alherai daban-daban a wannan sana’a ta waka ko masana’antar fina-finai, babu abin da zan ce sai alhamdulillah, sai dai in yi godiya ga Allah. Domin a Jihar Jigawa lokacin Gwamna Sule Lamido na samu alheri mai yawa, inda aka ba ni dama da hadin gwiwar Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar da ofishin Kwamishinan Watsa Labarai da na Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, na ziyarci kananan hukumomin jihar 27 don tsara wakokin Gwamna Sule Lamido da irin ayyukan da ya yi a kananan hukumomin. 

Ba zan manta ba a wancan lokaci bayan na yi aikin aka jarrabe mu da faduwar gini a kan mahaifana, inda da goyon bayan ofishin Jam’iyyar PDP, Shugaba da Sakatare da Kakakinta na wancan lokaci, aka turo motoci biyu daga Jigawa suka zo har garin Liman Katagum, domin su ga matsalar da ta same ni, kuma aka ba ni gudunmawar kayan abinci da sutura da kudi. Kuma na nemi taimako kan yadda zan gyara musu muhallin, saboda n ice kamar ginshikin gidan saboda da namiji daya ne a tsakanin mu ’ya’ya takwas na gidan. An ba ni tallafi na gyara musu dakuna biyu suka ci gaba da zama.

Ko akwai abin takaici da kika hadu da shi a sanadiyyar waka?

Eh, ba a rasawa, abubuwan suna da yawa. Amma ka san an ce ciki an yi shi ne ba domin tuwo kawai ba. Ko a nan Bauchi na hadu da kalubale daban-daban, hatta a gidan Gwamnatin Jihar Bauchi, sai dai mutum ya kawar da kai. Haka a cikin abokan sana’ata ta waka, a nan Bauchi akwai abin da aka yi min da ban taba tsammani ba. 

A cikin mawakan akwai ma wadanda suka yi wata kungiya cewa sai sun yi min dukan tsiya sai sun kashe ni. Ban san abin da na yi musu ba, illa sana’a ta hada mu, sannan an ba da wasu kudi da aka ce mu je mu raba, suka ce ba na cikinsu. Sai na ce to bari in je ni ma in nemi nawa, da na bi sawu aka ba ni, sai suka dauko motar ’yan sanda cewa wai na sace musu Naira dubu 250, don haka in ba su kudinsu ko su kashe maciji su cire wuyansa. Alhali a inda aka ba ni kudin an hada ni da ’yan sanda uku da wadansu mutum uku cewa su kai ni gida ni da mutanena. Kuma wadanda suka yi min haka dukkansu muna mutunci da su, wannan ya sa daga baya na katse hulda da su.  

Ga fahimtarki mece ce matsalar da take kawo cikas ga harkar waka a Najeriya?

Matsalar da take shafar harka ba ta waka kawai ba, ta komai ma, ita ce son kai da bakin ciki da kyashi da hassada da son zuciya kan abin da wani ya samu ko zai samu. Don me wane zai fi ni, ya kai wani matsayi sama da ni. Gaskiya akwai hassada da bakin ciki da sa ido cewa na riga wane fara waka, don me Allah zai daukaka shi a lokaci guda a tsakanin mawaka. To wannan ne yake kawo mana nakasu.

A fina-finai nawa kika fito?

Na fato a fim din ‘So Da Hauka’ a matsayin likita. Akwai kuma ‘Ta More Miji’ ko ‘Kan Ta ce,’ ina jin sun sauya masa suna. Akwai fim din fadakarwa kan shaye-shaye, inda na fito a matsayin matar Sani SK. Amma ban taba fitowa a matsayin jaruma ba, saboda na fi raja’a a harkata ta waka.

Ko kina wakokin da ake rerawa a fina-finai?

A gaskiya ba na wakar fim. Na fi yin wakokin siyasa da sarauta da kasida da na biki.

Yawanci mawaka sukan tsaya a jam’iyya daya, ke ma haka kike?

Eh, to ka san akan ce mawaki ba ya da alkibla, tunda dan kasuwa ne shi. A yanzu na fi raja’a a Jam’iyyar APC, ba don komai ba, sai saboda Gwamnan (Jihar Bauchi) ya yi min abin da ba zan manta da shi ba.

Me ya sa kika ce mawaka ba su da alkibla?

Abin da ya sa na ce ba su da alkibla, ai ka san haja ce a kasuwa, inda za ka sayar wa wane ka kai wa wane. Kuma duk wanda kake tunanin zai saya maka da mutunci kuma ya ga kimarka za ka yi harka da shi.

Ke nan in mawaki ya yi maka zambo ba mamaki wata rana ya yabe ka?

Shi ya fi sauki, Makera.

To ba ki ganin masu saurarenku su dauka cin amana ne?

Ba wai haka ba ne. Ai wani lokaci akwai abin da ake yi don duniya, musamman wanda ke tafiya da ’yan siyasa. Akwai abin da za ka yi, amma ba za su taba sanin kana yi ba. To amma idan bakinka ya yi kaifi, akwai kalmar da za ka fada ka gyara musu ko ka fada ka bata musu. To in ka yi musu batanci za su tuna baya cewa ba su kyauta maka ba a rayuwa. 

A duniya gaba daya, mawaka da matasa da mata suna taka rawa wajen tafiyar duk wani dan siyasa. To abin da ke jan hankulanmu shi ne a lokacin da ake tunanin yaya za a yi a cimma gaci, mu mawaka ake nema ana rike mu tamkar ’ya’yan wanda yake neman mukamin nan. To amma da zarar bukatarsa ta biya sai a watsar da mu. Alhali yana da kyau a sama mana matsayi ko a biya mana gurbin karatu saboda wadansu suna so su karo ilimi. 

Don haka muna jan hankalin ’yan siyasa da masarautu da kamfanoni da ’yan kasuwa su rika bai wa mawaka da ’yan fim hadin kai domin suna isar musu da sakonnin da su da mukarrabansu ba za su isar da su ba. Don haka su rika jan mu a jika suna nema mana kyakkyawar makoma a bangaren ilimi a rika rainon kwakwalenmu don cin gajiyar fasahar da muke da ita. Ya kamata a tuna rashin tallafa wa matasa masu tasowa ne yake haifar da miyagun abubuwan da suke faruwa na rikice-rikice da tashe-tashen hankula a sassan kasar nan.

Yaya batun kungiyarku ta mawaka da hanyar da za a inganta sana’ar waka?

Kowace sana’a ba ta iya yiwuwa gaskiya sai da shugabanci da kuma kungiyoyi. Domin kungiyoyin su ne cibiyar duniya da su ake tafiyar da kusan komai. Akwai kungiyoyi na majalisun dokoki na jihohi da na tarayya da ma na duniya baki daya. Saboda muna da Majalisar dinkin Duniya wadda kungiya ce ta hade kan duniya. Kuma a kowace harka ta shugabanci wajibi ne shugabanni su rika hakuri da danne zukatansu suna rike wadanda suke shugabanta. Su kuma ’ya’yan kungiyoyin kowa ya rika nuna biyayya ga shugabanni da kiyaye ka’idojin kungiyoyin.

A karshe mene ne sakonki ga mawaka da sauran jama’a?

Sakona shi ne jama’a su rika kyautata zato ga mu masu harkar waka da fim da siyasa musamman mu mata. Galibi jama’a suna munana zato ga mata ’yan fim, kuma yanzu abin ya fi muni ga mata ’yan siyasa saboda suna gwagwarmaya da maza. 

Ya kamata kowanenmu ya fahimci cewa in bai haihu ba, yana da ’yar uwa mace, in ya baci ’yar wani bai san abin da zai faru da tasa ba. Don haka a rika kyautata zato da fatan alheri ga matan da suke siyasa ko harkar waka da fina-finai. Kuma ina godiya ga masoyana na ciki da wajen Najeriya kan goyon bayan da suke ba ni.