Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci a rika yanke hukunci kan shari’o’in manyan laifuka cikin shekara guda.
A jawabinsa ga taron Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA), Buhari ya nemi a yi gyara domin kawo karshen umarni da hukunce-hukunce da masu karo da juna da kotuna ke bayarwa a kan shari’a daya.
Ya ce magance dadaddu da sabbin matsalolin kasa na bukatar a yi wa dokokin shari’a gyaran fuskata ta yadda za a kammala shari’ar manyan laifuka cikin shekara daya.
“Me zai hana a kayyade lokaci yanke hukunci a kan kowace Shari’a? Me zai hana a yi dokar da za ta wajabata kammala shari’ar manyar laifuka har a Kotun Koli cikin wata 12; Sauran shari’o’i kuma kar su wuce wata 15? Ina ganin hakan zai taimaka” inji shi ta baki mataimakinsa Yemi Osinbajo, wanda Babban Lauyan Najeriya (SAN) ne.
Ya shaida wa taron lauyoyin karo na 60 bukatar daukar kwararan matakai domin tunkarar matsalolin da ke tafe, inda ya bayyana bangarorin da ke bukatar a yi wa duba na tsanaki.
“Na yi amannar akwai bukatar yunkuri da kuma magance matsalolin da suka ci suka ki cinyewa a bangaren yanke hukunci.”
– Sanya wajen yanke hukunci
Jan kafar da kotuna ke yi wajen sauraron kararraki a baya na da ban takaici, kuma zai iya yin cikas ga cigaban al’umma, inji shi.
Ya ambato yadda ya shafe shekaru a yana neman adalci a Kotun Sauraron Karar Zabukan Shugaban Kasa bayan zabukan 2003, 2007 da 2011 kafin a yanke hukunci.
Sai dai ya ce bayan cin zabensa a 2015 ne kawai aka kammala shari’ar kokarfin zaben shugaban kasa cikin wata shida.
“Ni ba lauya ba ne amma na taba shigar da kara aka kayar da ni kuma an yi kara ta na kayar. Sai da na yi shekara biyu da rabi a gaban kotu, a shari’ata da Obasanjo daga 2003 ina neman zama shugaban kasa wanda wa’adinsa shekara hudu ne.
Ya ce a 2007 da ya shigar da kara sai da aka yi wata 20 a sharia’rsa da hukumar zabe ta INEC; Sannan karar da ya shigar a 2011 a shari’ar jam’iyyar CPC da INCE sai da aka yi wata takwas kafin a yanke hukunci.
“A karshe an kayar da ni a duk shari’o’in. Abin tambaya shi ne dalilin bata tsawon lokacin kafin yanke hukunci”.
Sai dai ya ce, “A 2019 an samu ci gaba, ba ni ke kara ba tawa aka kai a sharia’ar Atiku da Buhari kuma cikin wata shida aka kammala komai”.
– Yadda kotuna ke karo da juna
“Abu na biyu shi ne yawa da kuma cin karo da juna a umarni da hukuncin da kotuna ke yi.
“Kwanakin baya jam’yyata ta APC ta samu rikicin cikin gida. Amma cikin mako shida kafin in jagoranci taron jam’iyyar don magance batutuwan, kotuna a sassan kasar nan sun bayar da umarni akalla guda 10 masu karo da juna”, inji shi.