Wani mai taimaka wa harkokin addinin Musulunci kuma Shugaban Kamfanin Dab’i na Ibzar da ke garin Jos a Jihar Filato, Alhaji Ibrahim Abdullahi Muhammad ya yi kira ga gwamnatocin kasar nan kan su rika daukar alarammomi da mahaddata Alkur’ani Mai girma aiki.
Alhaji Ibrahim Abdullahi ya yi kiran ne lokacin da yake jawabi a wajen bude gasar karatun Alkur’ani Mai girma ta Karamar Hukumar Jos ta Arewa, karo na 33 a dakin taro na Babban Masallacin Jos.
Ya ce “Alkur’ani waraka ne ga kowane bangaren rayuwa. Don haka muna kira ga gwamnatocin kasar nan, a matakan tarayya da jihohi da kananan hukumomi su rika daukar wadanda suka haddace Alkur’ani a aikin gwamnati.”
Ya ce babu yadda za a yi mutum ya haddace Alkur’ani Mai girma, a ce masa jahili. Domin duk ilimin da mutum yake da shi, kuma kowanne fanni ya karanta, malamin da ya haddace Alkur’ani Mai girma yana da shi.
“Don haka idan gwamnatocin kasar nan suka dauki mahaddata Alkur’ani aiki, a bangarori za a warware matsalolin da suke damun kasar nan’,’ inji shi.
A jawabin shugaban shirya gasar ta Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Sheikh Aminu Sadis, ya ce dalibai 50 daga makarantun da suka fito daga karamar hukumar ne za su fafata a gasar.
Ya ce gasar karatun Alkur’ani da suke shiryawa a kowace shekara, ta yi sanadin bude makarantun haddar Alkur’ani da dama a karamar hukumar.