Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi kira da a rika ba wa ’yan sanda horo domin dakile matsalolin tsaro.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a taron tallafa wa matasan jihar wanda aka yi a Karamar Hukumar Karu a ranar Juma’a.
- Garkuwa: An ceto jami’an FRSC 26 a Nasarawa
- Majalisa ta dakatar da hadimin Gwamnan Nasarawa
- Sojoji sun fatattaki ’yan bindiga a Nasarawa da Biniwai
- #ENDSARS: An zakulo ‘yan sanda 16 da za a hukunta
Ya yi jan hankalin ne sakamakon rushe rundunar ’yan sandan SARS da Shugaban ’Yan Sanda na Kasa Mohammed Adamu ya yi.
“Sabon sauyin da muke son gani shi ne a samar da ’yan sanda da suka samu horo mai inganci, saboda rashin ingancin horo ne ya sa aka kai ga rushe SARS.
“Na san SARS sun samu horo a kan yadda za su kama ’yan fashi da sauran masu aikata manyan laifuka, wanda kuma ba kowane dan sanda ne yake da irin wannan horo ba.
“Tunda an rushe su, yana da kyau duk rundunar da za a kawo a tabbatar da an ba su cikakken horo kuma mai inganci”, cewar gwamna Sule.
Sai dai kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Kasa, Frank Mba, ya shaida wa manema labarai cewa sabuwar rundunar SWAT da aka kirkira, sai an gwada lafiyar kwakwalwar duk jami’in da za a dauka kafin a ba shi damar shi cikinta.