✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rana kamar ta yau

“Daniel ya amsa ya ce, albarka ga sunan Allah har abadan abadin, gama hikima da iko naSa ne; Yakan sake lokatai da kwanaki, Yakan tube…

“Daniel ya amsa ya ce, albarka ga sunan Allah har abadan abadin, gama hikima da iko naSa ne; Yakan sake lokatai da kwanaki, Yakan tube sarakuna, Yakan sarautar da sarakuna: Yakan ba da hikima ga masu hikima, ilimi kuma ga wadanda sun san fahimi:” (Daniel 2 : 20 – 21).

“Ni hikima na maida hankali mazaunina, ina binciken ilimi da hankali, Tsoron Ubangiji kin mugunta ne, Girman kai da alfarma da mugunyar hanya, da gautsin baki ina kin su. Shawara tawa ce, da sahihin ilimi: ni ne fahimi: ina da iko. Ta wurina sarakuna ke yin mulki, Mahukunta kuma suna yanke shari’a. Ta wurina mahukunta ke mulki, Hakimai kuma wato dukkan masu shari’ar duniya.” (Misalai 8 : 12 – 19).
Yau, a cikin tarihin wannan kasa tamu, muna ganin ikon Allah a fili. Watakila a daidai wannan lokaci ne muke kallon yadda ragamar mulki ke canja hannu; wato daga hannun mai girma Goodluck Ebele Jonathan zuwa ga sabon Shugaban kasa wanda muke da shi a yau ta wurin zaben da aka yi makonni kadan da suka gabata. A yau; muna gani a fili yadda Allah Yakan yi a yadda Yake so Ya yi, a kuma lokacin da Yake so Ya yi. A rana kamar ta yau, akwai masu murna domin sun samu shiga cikin masu mulki a wannan lokaci; akwai kuma da yawa wadanda zuciyarsu babu farin ciki ko kadan domin a dole za su bar fadar mulkin wannan kasa domin ba su iya sun ci zabe ba. Wadansu suna tunani game da abin da za su yi bayan sun bar shugabanci, ko kuwa domin ba su iske kansu cikin masu fada-a-ji ba yanzu. Wani lokaci ba abu ne mai sauki ba; musamman ma idan ba mu gane yadda Allah Yake aikinsa ba.
Daniel ya ba mu cikakken haske game da irin wadannan abubuwan da ke faruwa a lokaci kamar wannan
Allah Shi Yake iko da kuma hikima:
Maganar Allah na koya mana cikin Littafin Ishaya 55 : 8 – 9 cewa: “Gama tunaniNa ba tunaninku ba ne; al’amuranku kuma ba al’amuraNa ba ne; in ji Ubangiji, Gama kamar yadda sammai suna da nisa da duniya, haka nan kuma al’amuraNa sun fi naku tsawo, tunaniNa kuma sun fi naku.” Zai zama kuskure ne a gare mu idan muka yi tsammani cewa dole abubuwa su faru kamar yadda muka yi tunaninsu, ba lallai ba ne ko kadan. Allah ne ke da kalmar karshe game da dukkan abubuwan da ke faruwa da kowane dayanmu cikin wannan duniya. Shirin Allah ba lallai ne ya gamshe ka ba, domin kawai Shi Allah ne, Ya fi ka sanin abin da ke gaba. Mutane da yawa sun yi tsammani watakila Shugaba Goodluck zai ci zabe, amma sai aka wayi gari Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ci. Wannan bisa ga ikon Allah ne; mun rigaya mun yi dan bincike a kan shugabanci cewa, daga wurin Allah ne, kuma idan mutum ya iske kansa cikin matsayin manya, ko kuwa shugabanci kowane iri ne ma, mu sani AMANA ne daga wurin Allah, akwai ranar kawo lissafin duk abin da muka aikata yayin da Allah Ya ba mu zarafin shugabanci.
Allah ne Mai tube sarakuna kuma Shi ne Mai sarautar da sarakuna:
Mai yiwuwa a daidai wannan lokaci ne ake rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayin da yake kama ragamar mulki, Shugaba Goodluck Jonathan zai zama tsohon Shugaban kasa. Allah ne kadai ke da ikon tube sarakuna, Yana da iko kuma Ya sarautar da sarakuna kamar yadda yake so. Allah zai iya amfani da kowane mutum yadda Ya ga dama; babu wanda ya fi karfin Allah. Komai nufin mutum a cikin zuciyarsa, mu sani cewa Allah Shi Yake rike da zuciyar mutum kuma zai iya ya juya zuciyar mutum a koyaushe ya aikata nufinSa. Damuwa guda da nake gani cikin wannan kasa, mutane da yawa har cikin masu bin Yesu Kiristi ita ce, mutane ba su daukar lokaci su bidi nufin Allah game da abu; mutane sukan dauki yadda suke tsammani ya kasance. Maimakon mu dukufa wurin yin addu’a sai mu ba da karfi ga zargin shugabanni wadanda Allah Ya dora a bisanmu, wannan babu kyau ko kadan. Shugabanci ba abu mai sauki ba ne; duk abin da ka yi, akwai wadanda za su ce ba daidai ba; muddin ba su ne suka ba da shawara ba, muddin ba su ne suka yi ba. Idan har muna son ci gaba a wannan kasa, to akwai hanya guda – Addu’a, domin wadanda ke matsayin manya. Ba lallai ne sai wani ya gan ka kana addu’ar nan ba, Allah da Yake amsa addu’a Yana gani duka kuma zai albarkace ka bisa ga rike alkawarin da ka yi. A rana kamar haka; ya kamata mu zama masu godiya ga Ubangiji Allah domin salamar da muka samu a lokacin zabe, har ya kawo ga yau ranar da ake mika wa sabon Shugaba kasa ragamar mulki. Wannan sai mu sani alherin Allah ne kawai, Shaidan ya yi nufi ya hallaka mutane da yawa lokacin wannan zabe, amma Allah Ya riga shi; Ya kuma ba mu salamarSa har zuwa yau, wannan abin godiya ne sosai ga Allah. Dalilin godiya ga Allah na biyu kuwa shi ne, yadda Ya sa a cikin zuciyar Shugaban kasa mai barin gado, ya yarda da sakamakon zaben da aka yi ba tare da gardama ba ko kadan, wannan ba karamin alheri ba ne a matsayinmu na al’umma kasa daya. Sau da dama ba mu daukar lokaci mu gane jinkai na Allah da alheranSa masu yawa gare mu a zamanmu na ’yan kasa. A yau bisa ga nufi da kuma shirin Allah, Goodluck Jonathan zai sauka daga kujerar shugaban wannan kasa; haka kuma Allah zai dora Muhammadu Buhari bisa wannan kujerar kamar yadda Ya so Ya yi a wannan lokaci.
Mu roki Allah Ya ba wa shugabanninmu hikima da fahimi irin naSa:
Kowane mutum a cikin wannan kasa; musamman masu bin Yesu Kiristi, muna da aiki sosai domin ci gaban Najeriya. Babu mutumin da zai iya bugun kirjinsa ya ce ya san matsalar wannan kasa da yadda zai magance ta ba tare da neman nufin Allah ba, dole ne a matsayinmu na masu bin Yesu Kiristi mu rike hannuwan shugabanninmu cikin addu’a kowace rana domin su iya shugabanci daidai cikin tsoron Allah. Babu wanda yake da izini ya zargi shugaba da rashin yin adalci, muddin ba ka yi wa wannan shugaba addu’a domin Allah Ya bishe shi ya yi aiki daidai kamar yadda ya kamata ba. Abu daya da za ka iya yi wa shugabanka shi ne addu’a domin ya ci nasara cikin alkawarin da ya dauka a gaban Allah da kuma gaban mutane. Babu shakka dukkan shugabanni suna bukatar hikima da kuma ganewa idan har za su ci nasara cikin aikinsu; haka a namu sashin aikinmu ci gaba da taya su da addu’a, muna rokon Allah Ya taya su riko.
Mu gode wa Allah domin sabon Shugaban kasarmu Muhammadu Buhari, mu roki Allah Ya ba shi nisan kwana da lafiyar jiki domin ya iya aikata nufin Allah a cikin lokacin da Allah Ya ba shi. Haka kuma mu roki Allah domin Goodluck Jonathan yayin da ya bar kujerar mulki; bari Ubangiji Allah Ya ci gaba da tsare su daga miyagun mutane, su da iyalansu. Amin.

Ubangiji Ya taimake mu duka.