✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A mayar da tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara da aka tsige kujerarsa – Kotu

Kotun ta ce tsigewar da aka yi masa ba ta kan ka'ida

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin mayar da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara wanda aka tsige, wato Mahadi Aliyu Gusau kan kujerarsa.

Mahadi dai shi ne Mataimakin Gwamna zamanin mulkin tsohon Gwamna Bello Matawalle, wanda aka tsige saboda ya ki bin shi jam’iyyar APC daga PDP.

Mahadi da PDP ne suka shigar da karar suna kalubalantar tsige shi da Majalisar Dokokin Jihar ta yi a watan Fabrairun 2022.

Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang ya ce matakin da tsohon Gwamna Matawalle da kwamitin binciken da ya kafa wanda ya kai ga stige Mahadin raini ne ga batun da a lokacin yake gaban kotu.

Alkalin ya ce, “Muna bayar da umarnin a dawo da wanda yake kara (Mahadi Aliyu Gusau) kan kujerarsa a matsayin Mataimakin Gwamnan Zamfara tun daga ranar 8 ga watan Yulin 2021, lokacin da aka shigar da wannan karar.

“Kotu ta kuma jingine duk wani mataki da wadanda aka yi kara suka dauka a kan batun tsige tsohon Mataimakin Gwamnan Zamfara, lokacin da ake wannan shari’ar.”