Yayin da al’ummar Musulmi Najeriya da takwarorinsu a fadin duniya ke shirye-shiryen bukukuwan Babbar Sallah, Gwamnatin Jihar Filato takaita gudanar da sallar idi zuwa masallatan juma’a.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi ke daukar matakan takaita yaduwar annobar COVID-19 a yankunansu.
A ata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar mai dauke da sa hannun sakatarenta, Farfesa Danladi Atu, ta ce, “Dole ne kuma dukkan masallatan su tabbatar an bi dukkan matakan kariya daga cutar”.
Ta kuma shawarci tsofaffi da su zauna a gida domin su ne suka fi hadarin kamuwa da ita.
“Mun kuma yanke shawarar cewa dukkan wasu bukukuwa da wuraren shakatawa za su kasance a rufe.
“Sannan dole mutane su sanya takunkumi, musamman kananan yara da ake aikawa su kai abinci makwabta.
“Za mu dakatar da amfani da babura masu kafa uku na tsawon kwanaki biyu (ranakun Juma’a da Asabar) yayin da dokar Gwamnatin Tarayya ta hana fita daga karfe 10 na dare zuwa hudu na Asuba na nan daram”, inji sanarwar.
Gwamnatin ta kuma ce za ta tabbatar da an kiyaye dukkan matakan kariya a lokacin bukukuwan sallar don ganin jama’ar jihar ba su jefa kansu cikin hadari ba.