✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A magance kashe-kashe a Kudancin Kaduna

‘Yan Majalisar Wakilai daga Kudancin Kaduna sun bukaci a kara kaimi wajen hana kashe-kashen da ke faruwa a yankin. Sun yi rokon ne a taron…

‘Yan Majalisar Wakilai daga Kudancin Kaduna sun bukaci a kara kaimi wajen hana kashe-kashen da ke faruwa a yankin.

Sun yi rokon ne a taron da suka yi da ‘yan jarida a Abuja, ranar Laraba.

Mai tsawatarwa na masu rinjaye a majalisar, Gideon Gwani, ya ce, “A matsayinmu na masu wakiltar Kudancin Kaduna, ba tare da bambancin jam’iyya ba, mun yi tir da kashe-kashe da garkuwa da mutanen da ake yi a yankin.

“Mu wakilan ‘yan yankin ne da mazauna da duk wanda ya so yankin ba tare da bambacin kabila ko addini ko ra’ayin siyasa ko launin fata ba.

“Muna kira ga mutanenmu su zamo masu bin doka a duk da yanayin da muka samu kanmu ciki,” inji Gwani

Ya ce, suna allawadai da farmakin da ke salwantar da rayukan mutane tare da yin garkuwa da wasunsu.

“Hakan kazamin laifi ne kuma abun ki da ya saba wa dokar kasa ne”, inji shi. Saboda haka, ya zama dole a bi duk wata hanyar da ta dace don ganin an magance wannan fitina a dokance.” Inji Gwani